Daga Yunusa Isa, Gombe
Ƙungiyar Masu Sarrafa Shinkafa ta Jihar Gombe ta ƙarfafa alaƙa da rundunar ‘yan sandan jihar don tabbatar da tsaron ‘ya’yan kungiyar, da kakkaɓe ɓatagari da munanan iri a masana’antar.
Da yake tsokaci kan sabuwar dokar taƙaita zirga-zirgar dare da aka ɓullo da ita, yayin da ya karɓi baƙuncin jami’an rundunar ‘yan sanda masu yaƙi da muggan makamai SWAT a ofishinsa dake rukunin masana’antun Nasarawo, shugaban ƙungiyar na jiha Alhaji Lawan Yusuf ya yi ƙira ga ‘yan sanda da gwamnatin Jihar Gombe su yi la’akari da mambobinsu dake aiki da daddare.
“Mukan yi aiki har tsakar dare, kuma mambobinmu suna fuskantar ƙalubalen komawa ko fitowa daga gida yayin da jami’an tsaro ke tabbatar da ana bin wannan sabuwar doka, muna ƙira ga gwamnatin jiha da hukumomin tsaro musamman ku ‘yan sanda ku duba mambobinmu da za su iya zuwa aiki ko komawa gida daga aiki.
Shugaban yace za su samar da hanyar tantance ma’aikatan nasu na dare don tantance su cikin sauƙi.
Da yake yabawa gwamnatin jihar bisa samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa, Alhaji Lawan ya yabawa jami’an tsaro bisa yadda suke tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro a rukunin kamfanonin dama na ‘yan ƙasa baki ɗaya.
A nasa gudunmuwar, sakataren ƙungiyar Alhaji Shehu Muhammad Izala, yace ƙungiyar a shirye take ta samar da katin shaida ga ‘yan kungiyar dake aikin dare don tantancewa cikin sauƙi.
Yace “A irin waɗannan kamfanonin sarrafa shinkafa dake ɗauke da dubban matasa, dole ne a samar da jami’an tsaro don tabbatar da tsaro da doka da oda”.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban masaya shinkafa layin Onitsha, Alhaji Usman Ɗankwadan, yace kasancewar jami’an tsaro a rukunin kamfanonin, zai iya daƙile kasancewar masu baiwa ƴan garkuwa da mutane bayanai don aika-aikarsu.
Ya jaddada goyon bayansu ga shugaban ƙungiyar Alhaji Lawan Yusuf, yana mai cewa salon shugabancinsa ya yi tasiri wajen kawo sabbin ci gaba a ƙungiyar.
Kwamandan rundunar ta SWAT SP Ibrahim Tukur, ya baiwa masu sarrafa shinkafar tabbacin ci gaba da samun goyon bayan ‘yan sanda, yana mai cewa SWAT a shirye take don kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.
“Mun fito ne don tabbatar da doka da oda, kuma ina tabbatar muku cewa yadda na ga hadahada a wannan rukuni, yana da ban sha’awa sosai, kun samarwa matasa da dama abun yi, wanda a kididdigar da nayi ba zai gaza 5,000 ba. Don haka kun ɗauke wani gagarumin nauyi a kan gwamnati ta hanyar dauke matasan nan, kun sa sun zama masu amfanin kansu da tattalin arziki, kuma kun ba da gudummawa wajen rage aikata laifuka a jihar nan.”
SP Tukur ya buƙaci goyon baya da haɗin kan masu sarrafa shinkafar wajen yaƙar miyagun laifuka a rukunin kamfanonin dama Jihar Gombe baki daya, tare da tabbatar da cewa kasancwarsu a rukunin, zai kakkaɓe duk wasu ɓatagari a wurin.
A saƙonninsu na fatan alheri a madadin dattawa da matasan rukunin, Alhaji Ibrahim Ismail Jarmiya da Babawuro Ibrahim sun yabawa shugabannin ƙungiyar bisa yadda suka zage damtse wajen bunƙasa muradun mambobinsu.
Sun bada tabbacin bada haɗin kai da goyon baya ga shugabannin rukunin kamfanonin don ci gaban ƙungiyar.