…Yayinda Shugabannin Al’ummar Yankin Suka Yaba Da Ayyukan Yashe Madatsun Ruwa
Daga Adamu Abubakar, Gombe
Shirin Ingantawa da Zamanantar da Harkokin Kiwo (L-PRES), ya himmatu don zaƙulo damammakin da ake da su na kiwo a Gandun Dajin Wawa-Zange don inganta samar da abinci, da bunƙasa tattalin arziƙi, dama haɓaka sana’ar kiwo a Jihar Gombe.
Ko-odinetan shirin na L-PRES Farfesa Usman Bello Abubakar ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar al’ummar Wawa-Zange a wata ziyara da suka kai masa a ofishinsa.
Da yake bayyana takaicin yadda aka daɗe da yin watsi da harkar kiwo a Jihar Gombe, Farfesa Abubakar ya bayyana ƙudurin Gwamna Inuwa Yahaya na inganta harkar noma da kiwo don samar da wadataccen abinci tare da cin gajiyar arziƙin da wannan gandun dajin ke da shi, kasancewar yana ɗaya daga cikin gandun daji mafiya girma a Najeriya.
Shugaban na L-PRES ya bayyana cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar magance matsalar ƙarancin ruwa da ake fama da ita kowace shekara, wacce ke lalata wuraren kiwo da daƙile ci gaban sana’ar a yankin.
“Samar da ruwa wani muhimmin abu ne da muke mayar da hankali a kai, ana shirin jawo ruwa daga kogin Kupto da kuma tono albarkatun ruwan dake ƙarƙashin ƙasa. Binciken yanayin ƙasa ya tabbatar da yiwuwar cimma waɗannan buruka, kuma nan ba da jimawa ba za a tona manyan famfunan burtsatse. Wannar ingantacciyar hanyar samun ruwa za ta amfani dabbobi da al’ummomin dake kewaye, za kuma a yi ayyukan noman rani, lamarinda zai ƙarfafa gwiwar makiyayan da suka yi hijira saboda ƙarancin ruwa su dawo, wanda hakan zai ƙara haɓaka tattalin arzikin jiharmu”.
Farfesa Abubakar ya kuma bayyana cewa, ana shirin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da kafa cibiyar sarrafa madara, da kasuwa, da hotel, da dai sauran abubuwan buƙata a wurin.
“Bugu da ƙari, a ƙoƙarin mayar da wannan wurin ya zuwa cibiyar kiwon dabbobi mai inganci, muna shirin mayar da shi wurin shakatawa da yawon buɗe ido da zai janyo baƙi daga ciki da wajen kasar nan,” in ji shi.
Farfesa Abubakar ya jaddada muhimmancin rungumar hanyoyin kiwo na zamani, ya kuma buƙaci al’umma su goyi bayan shirin na L-PRES da sauran manufofi da tsare-tsaren gwamnati don samar da ci gaba dama bunƙasa tattalin arziki.
Ya buƙaci shugabannin al’ummar yanki su samar da zaman lafiya tare da haɗa kai da gwamnati don a samun zaman lafiya a jihar, yana mai ƙarfafa musu gwiwar su kai rahoton duk wani abu da suke zargin zai kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaba.
Tun farko a jawabinsa, Sarkin Fulanin Wawa-Zange, Malam Adamu Hassan wadda ya yi magana a madadin al’ummar Wawa-Zange, ya yaba wa shirin na L-PRES bisa namijin ƙoƙarin da yake yi na inganta harkar kiwo da bunƙasa tattalin arziƙi baki ɗaya.
Ya kuma yabawa gwamnati bisa gina asibitocin mutane dana dabbobi, da cibiyar tattara madara, da wuraren kiwon dabbobi na musamman, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen inganta kiwon dabbobi da ci gaban tattalin arziƙin al’ummar yankin.
“Mun zo nan ne don mu godewa gwamnati kan ayyukan da aka kammala da kuma waɗanda ake kan gudanarwa a dajin Wawa-Zange, waɗanda aka gudanar ƙarƙashin shirin L-PRES, musamman aikin yashewa da kuma toshe madatsun ruwa da aka yi kwanan nan, wanda ke tabbatar da samuwar ingantaccen ruwa ga mutane da kuma dabbobi, kuma yake amfanar da ɗokacin al’ummar dake kewaye da shi, tare da farfaɗo da muhalli”.
Ya ƙara da cewa “Mun daɗe muna fatan ganin wannan aiki a cikin al’ummarmu tun kafin a ƙirƙiro Jihar Gombe, amma duk ƙoƙarin da muka yi a baya bai yi nasara ba. Lokaci na ƙarshe da aka gyara mana madatsun ruwan nan shine tun muna tsohuwar Jihar Bauchi. Muna godiya ga gwamnatin Inuwa Yahaya data kawo mana ɗauki ta hannun wannan shiri na L-PRES”.