…Yana Mai Bada Tabbacin Yin Aiki Da Nagarta, Gaskiya Da Riƙon Amana
Daga Yunusa Isa, Gombe
Gogaggen ɗan jarida haifaffen Gombe, Kwamared Alhassan Yahya Abdullahi ya zama sabon Shugaban Kungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa (NUJ).
Da yake sanar da sakamakon zaɓen, Shugaban Kwamitin Zaɓe na Ƙungiyar, Kwamared Uche Nwigwe, yace Alhassan Yahaya ya samu ƙuri’u 436 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Kwamared Dele Atumbi wanda ya samu ƙuri’u 97, yayin da Garba Muhammad ya samu ƙuri’u 39.
Shugaban yace masu takaran sauran muƙamai sun yi nasara ba tare da hamayya ba.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsar da shi, Kwamared Alhassan Yahaya, ya yi alƙawarin inganta haɗin kai a tsakanin ƴaƴan ƙungiyar, da kyautata jin daɗi da walwalar ƴan jarida, da tabbatar da ‘yancin aikin jarida da kuma kare haƙƙin ƴan jarida.
Ya kuma yi alkawarin haɗa kai da gwamnati da masu ruwa da tsaki da sauran kafafen yaɗa labarai don ciyar da aikin jarida gaba a Najeriya.
Kwamared Alhassan Yahaya wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, ya miƙa godiya ga magoya bayansa tare da alƙawarin jagorantar ƙungiyar ta NUJ bisa gaskiya, adalci da riƙon amana.
Sabon shugaban ƙungiyar ta NUJ ya buƙaci goyon baya da haɗin kai daga dukkanin mambobin ƙungiyar don jagorantar ƙungiyar zuwa tudun mun tsira.
Ya kuma buƙaci duk ƴaƴan ƙungiyar su ƙara haɗa kai don cimma manufar ciyar da aikin jarida gaba a Najeriya.