Skip to content
Jewel Times
Menu
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Privacy Policy
  • Sample Page
  • Terms and Conditions
Menu

PDPn Gombe Ta Yi Watsi Da Takarar Yayari Tace Pantami ne Halastaccen Dan Takaran Gwamna

Posted on May 31, 2026May 31, 2026 by Jtimes

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta yi watsi da zaɓen fidda gwani da wani ɓangare a jam’iyyar ya gudanar, inda ta bayyana lamarin a matsayin haramtacce kuma barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na jiha, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya sanyawa hannu kuma ya miƙawa Jewel Times Hausa, jam’iyyar ta ce a ƙarƙashin jagorancin Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo (Talban Gombe) da Shugaban jam’iyyar na jihar, Manjo Janar Amnon Kalaye Kwaskebe (mai ritaya), jam’iyyar tana nan a kan bakanta cewa ta riga ta kammala duk zabukan fidda gwani a fadin jihar.

Da suke jaddada cewa jam’iyyar ta kasance “tsintsiya maɗaurinki daya ba tare da wani ɓangare ba a jihar,” jagororin sun bayyana cewa “ba za su zuba ido suna kallon wassu ɓatagari su haifar da ruɗani a cikin jam’iyyar ba.”

Don haka, PDP ta bayyana cewa ba ruwanta da wancan zaɓen da ya sabawa tsarin mulkin jam’iyyar, inda ta kwatanta su da “barazana ga haɗin kan jam’iyyar dama demokraɗiyya baki ɗaya.”

Shugabannin sun kuma jaddada cewa tsarin tantance ƴan takara na dukkan muƙaman siyasa ya riga ya kammala, wanda kuma ya tabbatar da da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takaran gwamna ɗaya tilo na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Dangane da haka, jam’iyyar ta yi ƙira ga duk masu ruwa da tsaki, mambobi, magoya baya, da sauran jama’a cewa “su yi watsi da harkokin irin waɗancan marasa kishin ƙasa, waɗanda ba sa son ci gaba da walwalar al’ummar Gombe.”

Wannan jawabi dai na zuwa ne a matsayin wani martani kai tsaye ga rahotannin dake yawo game da wani ɓangare na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki dake goyon bayan Ahmad Yayari a matsayin ɗan takaran gwamnan Gombe, wani mataki da shugabannin jam’iyyar na jihar suka fito fili suka soka tare da bayyana shi a matsayin aikin banza.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • PDPn Gombe Ta Yi Watsi Da Takarar Yayari Tace Pantami ne Halastaccen Dan Takaran Gwamna
  • Gombe PDP Affirms Pantami as Sole Gubernatorial Candidate, Dismisses Purported Yayari Candidacy
  • 2027: Over 1,500 Gombe Indigenes at KEDCO Endorse Dr. Jami Gwamna for Governor
  • President Tinubu Commissions Modern Infertility Centre at ATBUTH, Bauchi
  • Jamil Gwamna Hails Inuwa Yahaya’s Seven Years of Transformational Leadership in Gombe

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Human Capital Development
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme