Daga Yunusa Isa, Gombe
Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta bayyana damuwa kan yadda tace hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar (GOSIEC) ta gaza raba kayan gudanar da zaben ƙananan hukumomin da za a yi ranar Asabar a jihar.
Mukaddashin jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar Hon. Abdulrahman Buba Zaune da wani jigon jam’iyyar Alhaji Musa Sani Arawa, ne suka bayyana hakan yayin da suka ziyarci ofishin hukumar ta GOSIEC a yammacin jiya Juma’a don ganewa idonsu yadda ake raba kayan zaɓe a fadin jihar.
Suka ce basu ga wani alamun hadahadan zaɓe ba a ofishin sai jami’an tsaro kawai, don haka za su sanya ido don ganin ko hukumar za ta fitar da akwatunan zaɓe ko kuwa, suna masu cewa ba zasu lamunci rashin adalci da ɗauki ɗora ba a wannan karo.
Sun kuma yi barazanar cewa PDP zata dau matakan shariah kan hukumar zaɓen jihar matuƙar ba su ga akwati ba.
Hukumar ta GOSIEC dai ta sanya Asabar ɗin nan ne a matsayin ranar gudanar da zaɓukan na kananan hukumomi a jihar ta Gombe