Daga Yunusa Isa, Gombe
Biyo bayan gobarar data tashi a ɗaya daga cikin rumbunan adana magunguna na Jihar Gombe, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bada umarnin ɗaukar matakan gaggawa da suka haɗa da sake gina wani sabon rumbu, da sauran matakan maye gurbin magunguna da alluran rigakafin da suka salwanta.
Gwamnan ya ba da wannan umarni ne a yayin da ya kai ziyarar gani da ido a rumbun, yana mai cewa gwamnatin jihar na yin dukkanin mai yiwuwa don tinkarar lamarin.
Yace “Na umurci Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri ya gaggauta zuwa don duba irin matakan da ya kamata mu ɗauka, na magance faruwar hakan a nan gaba, tare da ɗaukan matakan gaggawa kan lamarin”.
Gwamnan ya kuma umarci hukumar kashe gobara ta jihar ta gudanar da bincike don gano musabbabin gobarar da kuma girman barnar data haddasa.
Yace gwamnatinsa tana ƙoƙarin tuntuɓar hukumomin bada agaji, don gaggauta maye gurbin magungunan da suka salwanta da sauran kayayyakin kiwon lafiya musamman alluran rigakafin cutar shan inna fiye da miliyan biyu da alluran rigakafin cutar sanƙarau miliyan ɗaya da ake shirin yiwa al’ummar jihar a watan Maris mai kamawa, musamman ƙananan yara don kare su daga cututtuka masu kisa.
Da yake zagayawa da gwamnan cikin rumbun, Kwamishinan Lafiya na Jihar Dr Habu Ɗahiru yace rumbun ba Jihar Gombe kaɗai yake amfana ba, ɗokacin jihohin arewa maso gabas ne ke amfana da shi.
Yace gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe 2:00 na dare wayewar garin yau Litinin, ta janyo asarar magunguna da kayayyakin jinya na fiye da Naira biliyan biyar.