Daga Yunusa Isa, Gombe
Shirin Zamanantar da Kiwo da bunƙasa Sana’ar Dabbobi a Jihar Gombe (L-PRES), ya shirya taron yini biyu ga malaman gona da likitocin dabbobi 33 kan dabaru da hanyoyin bunƙasa kiwon dabbobi na zamani a jihar.
A jawabinsa na maraba, Ko’odinetan shirin na L-PRES a jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, yace an shirya taron bitar ne da nufin ƙarfafa gwiwar likitocin dabbobi da malaman gonan kan sabbin dabaru da hanyoyin zamanantarwa da inganta harkar kiwo a jihar.
Ko’odinetan yace horon wanda shi ne irinsa na farko a jihar, zai kuma bunƙasa dabarun sadarwa ga mahalarta taron don sadarwa yadda ya kamata da kuma yaɗa bayanai ga manoma da makiyaya.
Farfesa Bello Abubakar ya bada tabbacin cewa za a ci gaba da shirya irin wannan horo don faɗakar da manoma dabarun kiwo na zamani.
Yace a ƙoƙarinsa na inganta kiwo a Jihar Gombe, shirin na L-PRES yana gyara kasuwannin dabbobi na Kashere, da Leggal da Bajoga, yana mai tabbatar da cewa a albarkacin shirin, Jihar Gombe ce ke da asibitin dabbobi na zamani da yafi kowanne a Arewa.
Farfesa U.B. Abubakar ya ƙara da cewa jihar ce kan gaba wajen aiwatar da shirin na L-PRES a tsakanin jihohi 20 da ake aiwatarwa da shi a ƙasar nan.
Ya yabawa gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na kawo shirin Jihar Gombe.
Da yake jawabi yayin da yake ƙaddamar da taron bitar, kwamishinan noma, kiwo da ƙungiyoyin gama kai na jihar Dr Barnabas Malle, ya buƙaci mahalarta taron su mai da hankali sosai kan horon tare da yaɗa ilimin ga manoma da makiyaya na yankunansu.
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Dakta Ibrahim Yakubu Usman, yace Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na da sha’awar harkokin noma da kiwo, hakan yasa ya mayar da hankali wajen inganta sashin.
Yace, a kwanakin baya ne gwamnan ya ƙaddamar da shirin allurar rigakafin cututtukan dake kashe dabbobi a jihar, kana ya bada fili ga gwamnatin tarayya don gina asibitin dabbobi kan hanyar Liji domin inganta kiwo a jihar.
Kwamishinan ya yabawa shirin na L-PRES a Jihar Gombe bisa shirya wannan horon, yana mai bayyana shi a matsayin abinda ya dace kuma ya zo akan gaɓa.
Mahalarta taron da aka zaɓo daga dukkanin ƙananan hukumomin jihar 11, an gabatar musu da makaloli da ƙasidu daban-daban kan dabarun kiwo dabbobi na zamani.