Skip to content
Jewel Times
Menu
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Privacy Policy
  • Sample Page
  • Terms and Conditions
Menu

2027: Bala Tinka ya Zama Dan Takaran Gwamna na ADC a Gombe

Posted on May 24, 2026 by Jtimes

…Ya Samu Ƙuri’u 104,47 Inda ya Kada Dokaji Mai Kuri’u 6,443

Daga Yunusa Isa, Gombe

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Gombe ta ayyana Dr. Bala Bello Tinka a matsayin ɗan takaranta na gwamna a babban zaben 2027, bayan nasarar daya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar kai tsaye da aka gudanar a faɗin gundumomi 114 na jihar.

Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwani na ADC, Farfesa David Agbu ne ya sanar da sakamakon a Gombe jiya asabar, inda ya tabbatar da cewa Dr. Tinka ya samu kuri’u 104,407 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Adamu Muhammad Dokaji, wanda ya samu kuri’u 6,443.

Farfesa Agbu yace “Bayan ya cika sharuɗan da kundin tsarin mulkin ADC da kuma ka’idojin zaɓen jam’iyyar suka tanadar, Kwamitin ya ayyana Dr. Bala Bello Tinka a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya ayyana shi ɗan takaran gwamna na ADC a zaɓen 2027 a Jihar Gombe,”

Da yake tsokaci kan yadda aka gudanar da zaɓen, wanda aka fara daga ranar 21 zuwa 23 ga wannan wata na Mayu, Farfesa Agbu ya yaba da yadda aka yi zaɓen cikin yanayin zaman lafiya a faɗin jihar. “Kwamitin ya sanya ido sosai kan yadda ake tantancewa da kaɗa ƙuri’a, kuma mun gamsu cewa an gudanar da zaɓen fidda gwanin cikin kwanciyar hankali. Zaɓen ya kasance cikin ‘yanci, adalci, da kuma gaskiya,” in ji shi.

Ya miƙa goron gayyata ga duk wadda bai gamsu da zaɓen ba da ya bi hanyoyin da suka dace don neman kadu. “Muna ƙira ga duk wani memba da bai gamsu da sakamakon da aka sanar ba, ya kai korafi gaban kwamitin ɗaukaka ƙara na jam’iyyar don ƙalubalantar sakamakon a hukumance,” in ji shi.

Ƙuri’un da aka kaɗa sun nuna rinjayen Dr. Tinka ya samu a kananan hukumomi 11 na jihar kamar haka: A Ƙaramar Hukumar Akko, Tinka ya samu kuri’u 13,785 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 117.

A Ƙaramar Hukumar Balanga, Tinka ya samu kuri’u 9,530 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 729. A Ƙaramar Hukumar Dukku, Tinka ya samu kuri’u 6,900 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 71.

A Ƙaramar Hukumar Billiri, Tinka ya sami kuri’u 8,569 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 601. A Ƙaramar Hukumar Kaltungo, Tinka ya samu kuri’u 4,534 idan aka kwatanta da 4,059 da Dokaji ya samu.

A Ƙaramar Hukumar Kwami, Tinka ya samu kuri’u 10,444 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 64, yayin da a Shongom Tinka ya samu kuri’u 6,158 Dokaji ya samu kuri’u 406.

A Ƙaramar Hukumar Funakaye, Tinka ya samu kuri’u 8,480 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 99. A Ƙaramar Hukumar Nafada, Tinka ya samu kuri’u 5,488 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 152.

A Ƙaramar Hukumar Gombe, Tinka ya samu kuri’u 19,242 inda Dokaji ya samu kuri’u 51. A Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba, Tinka ya samu kuri’u 10,943 yayin da Dokaji ya samu kuri’u 94.

Bayan sakamakon zaɓen gwamna, kwamitin ya kuma bayyana ‘yan takaran jam’iyyar a sauran mukamai. Mustapha Aliyu ya yi nasara a matsayin dan takarar Sanatan Gombe ta Arewa, Abdullahi Idris Umar a matsayin ɗan takaran Sanatan Gombe ta tsakiya, da Mela Audu Nunge a matsayin ɗan takararn sanatan Gombe ta Kudu.

Haka kuma an tabbatar da jerin ‘yan takaran majalisar wakilai dana jiha.

Daga cikin wadanda aka zaba don neman kujerun majalisar tarayya akwai Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi (Akko), Hon. Usman Sa’ad Aliyu (Yamaltu-Deba), Hon. Ali Babayo Maigoro (Gombe/Kwami/Funakaye), Hon. Abdullahi Elrashid (Dukku/Nafada), Hon. Kabir Abubakar (Kaltungo/Shongom), da Hon. Sadik Abubakar Adamu (Balanga/Billiri).

Biyo bayan kammala zaɓen fidda gwanin, yanayin siyasa a Gombe yana ƙara ɗaukar harama, yayinda ake ƙara tinkran zaɓen 2027.

Dr. Tinka na shirin fafatawa da ƴan takaran da dama, ciki kuwa har da ɗan takaran jam’iyyar APC, Dr. Jamil Isiyaku Gwamna, da kuma wanda za a zaɓa daga jam’iyyar PDP nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Gov Inuwa Intensifies Livestock Modernisation as Gombe L-PRES Trains 168 Cooperative Leaders
  • 2027: Bala Tinka ya Zama Dan Takaran Gwamna na ADC a Gombe
  • 2027: Pantamiyya Movement Brothers Backs Gwamna, Urges APC Unity
  • 2027: Bala Tinka Emerges ADC Guber Candidate in Gombe
  • Experts Task Gombe Residents on Regular Antenatal care as Panacea to Preeclampsia

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme