Daga Yunusa Isa, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa ‘ya’yan jam’iyyar APC daidai suke, kuma za su samu haƙƙoƙi da kulawa daidai wa daida ba tare da la’akari da jimawarsu a jam’iyyar ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da Tsohon Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Gombe, Hon. Barista Rambi Ibrahim Ayala ya karɓi katin jam’iyyar APC a gundumarsa ta Ɓiliri ta Kudu.
Gwamna Inuwa wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Muhalli, Ruwa da Gandun Daji, Muhammad Sa’idu Fawu, yace “Dawowar Hon. Rambi cikin APC ya ƙarawa jam’iyyarmu ƙarfi da armashi a yankin Tangale Waja, muna fata ka dawo kenan, kuma za ka bada gudummawarka yadda ya kamata don nausa APC gaba a Tangale Waja da Jihar Gombe”.
Gwamnan ya bayyana sauya shekar ta Hon Rambi a matsayin nasara ga demokraɗiyya, yana mai ƙira gareshi ya saki jiki ya bada cikakkiyar gudunmawarsa don ci gaban jam’iyyar.
A nasa jawabin a madadin Jam’iyyar APC ta jiha, Hon Isiyaku Abdullahi (Jarman Akko), yace jam’iyyar ta cika da jin daɗi da komawar Rambi Ayala cikinta, yana mai bayyana shi a matsayin jigo a fagen siyasar Tangale Waja.
A saƙonninsu na fatan alheri, shugabannin ƙananan hukumomin Ɓiliri, Kaltungo da Shongom Madam Eglah Idris da Hon Iliya Sulaiman da kuma Hon. Fatima Binta Bello, sun bayyana farin ciki da sake samun Rambi Ayala a cikin APC, inda suka tabbatar masa shi da magoya bayansa cikakken goyon bayansu wajen ciyar da jam’iyyar gaba.
A jawabansu yayin gabatar da sabon katin jam’iyyar ga Hon Rambi Ayala, shugaban jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ɓilliri Isiyaka Zakari da takwaransa na gundumar Ɓiliri ta Kudu Andrew Nayako wanda sakatarensa Yushau Shehu ya wakilta, sun bayyana cewa APC gida ce ga Hon Rambi, suna masu jaddada tasirinsa na ganin jam’iyyar ta yi nasara a dukkan matakai a 2027.
A nasa jawabin, Hon Barista Rambi Ibrahim Ayala, yace “Mun yanke shawarar komawa APC ne don dafawa ƙoƙarin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na samar da ribar demokraɗiyya ga al’ummarmu a faɗin Jihar Gombe”.
Hon Rambi ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ya zamanantar da Gombe, yana mai bada tabbacin bashi goyon baya kan ƙoƙarinsa na nausa Jihar Gombe ga tudun mun tsira.
Bikin ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki, waɗanda suka cika da farin ciki suna masu tarbar tsohon ɗan majalisan dokokin na Jihar Gombe zuwa APC.