…Yayinda Ko-odinetan L-PRES Na Gombe Ya Jaddada Ƙudurin Gwamnati Na Kawo Sauyi A Harkokin Kiwo A Jihar Gombe
Tawagar ƙungiyoyi masu alaƙa da harkar kiwon dabbobi a Jihar Gombe sun yaba da yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta mayar da hankali wajen bunƙasawa da zamanantar da sana’ar kiwo a jihar.
Kungiyoyin sun yi wannan yabon yayin wata ziyarar da suka kai wa ko-odinetan shirin zamanantar da harkokin na kiwo (L-PRES) na Gombe, Farfesa Usman Bello Abubakar a ofishinsa.
Da suke jawabi a madadin mambobinsu, shugaban ƙungiyar dillalan shanu Malam Abubakar Adamu, da shugaban ƙungiyar masu sayar da awaki da tumaki ta jihar Gombe Ahmed Isa, da kuma shugaban ƙungiyar masu sayar da abincin dabbobi Inuwa Maikano, sun yabawa gwamnatin bisa ƙoƙarin da take yi na inganta kiwon dabbobi a ƙarƙashin shirin na L-PRES duba da rawar da yake takawa ga masu ruwa da tsaki.
Sun kuma yi godiya ga shirin na L-PRES da ya jawo su jiki don damarwa da su a ayyukansa, suna masu alkawarin ba da cikakken haɗin kai da goyon baya ga shirin na L-PRES da Gwamnatin Jihar Gombe ƙarƙashin Gwamna Inuwa Yahaya don bunƙasa harkar kiwo a Jihar Gombe baki ɗaya.
Shuwagabannin sun yaba da aikin gyaran madatsun ruwa a Gandun Dajin Wawa-Zange, da gina asibitocin kula da dabbobi, da gyaran kwaataa (mayankan dabbobi), da tona rijiyoyin burtsatse don samar da ruwan sha ga jama’a da dabbobi.
Suka ce waɗannan ayyuka da aka gudanar za su taimaka matuƙa wajen inganta sana’ar kiwo a faɗin jihar.
A nasa jawabin, Ko-odinetan shirin na L-PRES a Gombe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya yabawa ƙungiyoyin bisa hadin kan da suka nuna ƙarƙashin inuwa guda don nuna goyon bayansu ga shirin na L-PRES.
Ya jaddada ƙudurin shirin na kawo sauyi ga harkokin kasuwancin dabbobi a Jihar Gombe don ya dace da ka’idojin ƙasa da ƙasa.
Farfesa Abubakar ya danganta nasarar shirin na L-PRES a Jihar Gombe da goyon baya da kuma jajircewar Gwamna Inuwa Yahaya, da nufin yin amfani da ƙarfin da jihar ke da shi a fannin kiwo don bunƙasa tattalin arziƙinta.
Yace ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ƙarƙashin shirin L-PRES, ta gina dakin gwaje-gwaje da duba lafiyar dabbobi na zamani a Kasuwar Shanu ta Gombe don inganta harkokin kiwo da lafiyar dabbobi.
Haka kuma ana ci gaba da gyare-gyare a kwaatan Gombe, da Bajoga, da kuma Kumo a ƙoƙarin sake fasalin fannin.
Farfesa Abubakar ya buƙaci ƙungiyoyin su marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, yana mai cewa nan ba da daɗewa ba za a faɗaɗa harkokin kasuwancin na dabbobi, yayinda ake ci gaba da tsare-tsaren gina babbar kasuwar dabbobi ta zamani ta duniya da kuma kwaataa mai ɗauke da kayan aiki na zamani don bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe da inganta rayuwar masu ruwa da tsaki.
Ya ƙara da cewa wannan shine karon farko da wani gagarumin shirin inganta kiwon dabbobi ya zo jihar, kuma nan ba da jimawa ba shirin zai tsara masu cin gajiyar ayyukansa don tallafawa masu kiwon dabbobi. Ya buƙacesusu su haɗa kai domin mambobinsu wadanda suna cikin manyan masu ruwa da tsaki suma su amfana.
“Ganin wannan sabon ci gaban da aka samu a fannin, da bukatun wasu ƙasashe na a samar musu da naman awaki, yasa gwamnati ta shiga aikin inganta cibiyoyi da kayan aikin da suka dace da buƙatun ƙasa da ƙasa ta yadda za mu yi gogayya da kyau a fagen kiwo a duniya.” Inji shi.
Farfesa Abubakar ya ƙara da cewa kasancewar Jihar Gombe a tsakiyar yankin Arewa Maso Gabas kuma Allah ya albarkace ta da ɗimbin arziƙi, yasa ta kasance jiha mafi cancanta a ɓangarori da dama. Ya kuma ba su tabbacin cewa za a yi amfani da damammakin da ake da su wajen inganta samar da abinci, da bunƙasa tattalin arziki da ci gaba a yankin.
Ko’odinetan ya jaddada muhimmancin rungumar hanyoyin kiwo na zamani, sannan ya buƙaci ƙungiyoyin su baiwa shirin na L-PRES da sauran tsare-tsaren gwamnati goyon baya don ci gaban jihar.
Jami’in kula da shirin ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Inuwa Yahaya, ta duƙufa wajen ganin an magance rikicin manoma da makiyaya da kuma daƙile matsalar rashin tsaro a jihar ta hanyar tattaunawa, da alkinta wuraren kiwo da burtalolin shanu, da kuma haɗa kan al’umma da masu ruwa da tsaki.
Farfesa U. B. Abubakar ya bayyana cewa sabon ɗakin gwaje-gwajen cututtukan dabbobin da aka kammala a asibitin dabbobi dake kasuwar shanu ta Tashar Dukku, zai taimaka matuƙa wajen inganta lafiyar dabbobi da share fagen fitar da lafiyayyen nama zuwa ƙasashen waje irin su Qatar dake buƙatar naman awaki daga Najeriya.
Ya ci gaba da cewa, “Wanan shi ne karo na farko da aka fara kawowa Jihar Gombe tallafi don inganta kiwon dabbobi, don haka dole ne mu tabbatar da cewa mun yi amfani da damar da muka samu wajen kawo sauyi a fannin kiwo”, yana mai jaddada cewa shirin na L-PRES zai ƙarfafa sana’o’in dake da alaƙa da kiwo don haɓaka ayyuka da ribar da suke samu da kuma rage musu asara,
Ko-odinetan ya bayyana shirye-shiryen ƙididdige duk masu ruwa da tsaki a harkar dabbobi da nufin tallafa musu, yana mai cewa “Za a samar da babbar kasuwar dabbobi ta duniya da kwaataa ta zamani, tare da mutunta tanade-tanaden addini da al’adun al’ummar Jihar Gombe,” in ji shi.