Skip to content
Jewel Times
Menu
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Sample Page
Menu

Gwamnan Gombe Ya Kaddamar Da Rabon Tallafi Karo Na 17 Ga Marassa Galihu 214,500

Posted on March 26, 2024March 26, 2024 by Jtimes

Daga Yunusa Isa,

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da wani sabon rukuni na rabon tallafin kayan abinci karo na 17 ga marassa galihu 214,500, wadda za a yi a runfunan zaɓe 2,218 dake mazaɓu 114 na jihar.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon a Filin Wasa na Pantami, gwamnan yace gwamnatinsa ta duƙufa wajen tallafawa al’ummar jihar musamman talakawa da marasa galihu.

“Wannan rabo ya nuna cewa sadaukarwar da muke yi wajen taimakawa al’ummarmu dake cikin mawuyacin hali wani dabi’a ne na wannar gwamnati, kama daga lokacin annobar corona zuwa cire tallafin man fetur a baya-bayan nan, mun ɗauki matakan ragewa al’ummah raɗaɗin halin da suke ciki”.

Ya buƙaci kwamitin rabon tallafin ya tabbatar da adalci a aikinsa, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci cin hanci da rashawa ko wane nau’i ba.

“Burinmu shi ne mu samawa al’ummarmu damar dogaro da kansu ta fuskar samarwa kansu abinci, ba wai a ko da yaushe su yi ta jiran irin wannan tallafin da ba zai ɗore ba”.

Da yake ƙira ga al’ummar jihar su ci gaba da taimakawa juna, Gwamna Inuwa ya buƙacesu su yi wa Jihar Gombe addu’a da Najeriya baki ɗaya.

Tun da farko a nasa jawabin shugaban kwamitin rabon kayan abincin kuma mataimakin gwamnan jihar Dr Manassah Daniel Jatau wanda shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Abubakar Inuwa Kari ya wakilta, yace gwamnatin jihar tana sane da irin matsalolin tattalin arziƙin da al’ummar jihar ke fuskanta musamman na ƙarancin abinci.

Yace an kafa ƙananan kwamitocin masu ruwa da tsaki a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi, don tabbatar da rabon kayan abincin cikin tsanaki.

Ya yabawa al’ummar jihar bisa natsuwa da bin doka da oda da suka nuna, duk da ƙalubalen da ake fuskanta na matsin tattalin arziƙi.

A jawabinsa na godiya a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Mai Martaba Sarkin Gombe Dr Abubakar Shehu Abubakar na 3, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa yadda a kullum yake taimakon marasa galihu musamman a wannan lokaci na taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Ya yi ƙira ga sauran ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙamai su yi koyi da wannan karimci na gwamna Inuwa.

Tallafin abincin na wannan karo ya ƙunshi taliya, shinkafa da kuma masara.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Parents Encouraged to Support Nursing Students
  • Gombe’s Infrastructure Push: Works Commissioner Highlights Benefits of Key Projects
  • Gombe Govt Efforts Paying Off as Farmer-Herder Clashes Minimised — Agric Commissioner
  • Muhammadu Buhari Industrial Park Takes Shape with 12 Companies on Site, 14 on Queue
  • Gombe Governor Commissions POWA Model School in Sum, Bauchi State

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2025 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme