Skip to content
Jewel Times
Menu
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Privacy Policy
  • Sample Page
  • Terms and Conditions
Menu

Atiku Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyar ADC da Kuri’u 139,334 a Gombe

Posted on May 26, 2026 by Jtimes

Daga Yunusa Isa, Gombe

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya samu gagarumar nasara a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, inda ya lallasa abokan takararsa, Rotimi Amaechi da Muhammad Hayatuddeen Adamu da tazara mai ɗimbin yawa.

Da yake sanar da sakamakon a hukumance bayan tattara sakamakon ƙananan hukumomi 11 na jihar, Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwanin na ADC a Jihar Gombe, Farfesa David Agbu, ya tabbatar cewa Atiku ya kada abokan karawar tasa biyu Amaechi da Hayatuddeen warwas.

Bisa ga alƙaluman da Farfesa Agbu ya bayyana a hukumance, Atiku ya samu nasara da kuri’u 139,334. Yayinda Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 1,150, Hayatuddeen kuwa ya zo na ƙarshe da ƙuri’u 465.

“Bayan samun mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa, kuma ya cika dukkan sharuɗan da doka ta tanada, kwamitinmu ya gamsu cewa Atiku Abubakar ne ya samu mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa, kuma mun bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar ADC a Jihar Gombe,” in ji Farfesa Agbu.

Haka zalika, shugaban kwamitin ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen cikin tsari, yana mai cewa “Zaɓen ya kasance cikin lumana, gaskiya, adalci, da kuma nagarta a dukkanin gundumomi 114 na jihar”.

Yanayin ƙuri’un da aka kaɗa ya nuna yadda zaɓen ya kaya a ƙananan hukumomi 11 inda Atikun ya mamaye jihar:

A Ƙaramar Hukumar Gombe: Atiku ya samu ƙuri’u 27,800, yayin da Amaechi ya samu 376, Hayatuddeen kuma ya samu 40.

A Yamaltu-Deba: Atiku ya lashe kuri’u 20,367, inda ya bar Amaechi da kuri’u 5, Hayatuddeen kuma 4.

A Ƙaramar Hukumar Akko ma Yanayin bai canza ba, inda Atiku ya samu ƙuri’u 17,218, yayin da Amaechi ya samu 308, Hayatuddeen kuwa ya samu ƙuri’u 50.

Atiku ya kuma samu makamanciyar wannar nasara da gagarumar tazara a sauran ƙananan hukumomin jihar kamar haka:

Kwami: (Atiku 13,973; Amaechi 11; Hayatuddeen 5).

Funakaye: (Atiku 13,323; Amaechi 14; Hayatuddeen 5).

Kaltungo: (Atiku 10,853; Amaechi 28; Hayatuddeen 16).

Balanga: (Atiku 8,958; Amaechi 270; Hayatuddeen 80).

Billiri: (Atiku 8,086; Amaechi 208; Hayatuddeen 202).

Dukku: (Atiku 7,636; Amaechi 38; Hayatuddeen 27).

Shongom: (Atiku 5,678; Amaechi 51; Hayatuddeen 21).

Nafada: (Atiku 5,416; Amaechi 21; Hayatuddeen 5).

Wannar gagarumar nasara ta sake tabbatar da cewa Gombe sananniyar cibiyar magoya baya ce ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasar.

Wannan rinjaye da Atiku ya samu a jihar ta yi kama da wacce ya samu a babban zaɓen da ya gabata, inda ya doke shugaba Bola Ahmed Tinubu, da gagarumar tazara.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Atiku Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyar ADC da Kuri’u 139,334 a Gombe
  • Atiku Sweeps ADC Primary with 139,334 Votes in Gombe
  • Gombe Revolutionizes, Boost Livestock Sector, Trains 173 Farmers on Artificial Insemination
  • Gov Inuwa Intensifies Livestock Modernisation as Gombe L-PRES Trains 168 Cooperative Leaders
  • Gombe PDP Gubernatorial Aspirants Reject Pantami’s Defection Move, Warn Against Primaries Infiltration

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme