Daga Jibrin Hussaini Kundum, Bauchi
Ƴaƴan sarakuna a Najeriya sun buƙaci Gwamnatin ƙasar ta samarwa sarakuna aiki a hukumance a kundin tsarin mulki.
Wata gidauniyar ƴaƴan sarakunan Arewa mai suna ‘In Ka Ji Tambura’ ta buƙaci gwamnatin tarayya ta samarwa sarakuna gurbi a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan.
Buƙatar hakan ta fito ne ta bakin Magatakardar Gidauniyar Prince Mahmud Aminu Adamu Jumba, a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Bauchi.
Yace “Ko shakka babu ba wani ɗan basaraken arewacin Najeriya da zaiyi farin ciki da abun dake faruwa a Jihar Kano sakamakon taƙaddamar sarautar sarki mai daraja ta ɗaya”.
Mahmoud Adamu Jumba ya ƙara da cewa “Ba za mu lamunci abin da zai taba kimar iyayen mu sarakuna ba”.