Daga Yunusa Isa, Gombe
An jaddada buƙatar al’ummar Jihar Gombe su mutunta aƙidar juna, da kare hakkin bil-adama tare da taimakawa juna.
Babban jami’in da ya gabatar da maƙala Dr Obadiah Samuel na Jami’ar Jos ne ya jaddada buƙatar hakan yayin wani taron tuntuɓa na masu ruwa da tsaki kan haƙƙin ɗan-adam da mutunta addinan juna, wanda Tekan Peace Desk ta shirya a Gombe.
Da yake gabatar da maƙala mai taken “Mu Fahimci Matsalar Rashin Mutunta Addini da Tasirinsa Kan Kare Haƙƙoƙin Ɗan-Adam” da kuma wata maƙalar mai taken “Hanyoyin Samar da Mafita Don Kare Haƙƙoƙin Ɗan-Adam”, Obadiah yace girmama addinan juna yana da nasaba da mutunta aƙidar wassu da kuma gujewa duk wani abu da ka iya tunzurasu.
Da yake ƙarfafa gwiwar al’ummar jihar su ci gaba da zama ’yan uwan juna, jami’in yace haƙuri da girmama addinan juna yana kawo zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Dangane da kare haƙƙin ɗan-adam, Dr Obadiah yace yarjejeniyoyin ƙasa, dana nahiyoyi dana ƙasa da ƙasa sun amince da yancin rayuwa, da yancin addini ga kowa, yana mai cewa ya zama wajibi ga ɗaiɗaikun jama’a da kasashe su mutunta tare da kiyaye waɗannan haƙƙoƙi.
Ya buƙaci mahalarta taron su zama jakadun zaman lafiya ta hanyar isar da ilimin da suka samu a yayin taron ga waɗanda basa wurin.
Wassu daga cikin mahalarta taron da suka haɗa da Lami Andrew da Ali Alola Alfinti, sun bayyana jahilci da fatara da son zuciya irin na siyasa da tsattsauran ra’ayi a matsayin manyan ababen dake haddasa rashin mutunta addinan juna a jihar.
Sai dai sun bayyana ƙauna, da ilimi, da wayar da kan jama’a da fahimtar juna da kuma yaƙi da fatara a matsayin hanyoyin magance rashin girmana addinan juna da take haƙƙin ɗan-adam. Sun kuma ba da tabbacin isar da ilimin da suka ƙaru da shi zuwa ga wassu.
Tekan Peace Desk tare da tallafi daga Brot da Tarayyar Turai suna aiwatar da wani shiri ne mai take ‘Addini don Aminci’ a wassu garuruwa shida; biyu a kowace karamar hukuma na Kwami, da Yamaltu Deba da kuma Ɓillliri.
Shirin yana maida hankali ne wajen baiwa masu ruwa da tsaki damar inganta zaman lafiya, da kare haƙƙin ɗan-adam, da demokraɗiyya da kuma mutunta addinan juna a Najeriya.
Waɗanda da suka halarci taron sun haɗa da ƙungiyoyin al’umma dana addinai dana fararen fula, da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai, da jami’an gwamnati da hukumomin tsaro da kuma masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama.