Skip to content
Jewel Times
Menu
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Sample Page
Menu

Shirin L-PRES Ya Horar Da Makiyaya 114 Dabarun Sarrafawa Da Alkinta Harawa A Gombe

Posted on March 2, 2024March 2, 2024 by Jtimes

Daga Yunusa Isa, Gombe

Shirin zamanantarwa da bunƙasa harkokin kiwo wato (L-PRES) ya horar da makiyaya 114 a Jihar Gombe dabarun sarrafa karmami na zamani don inganta sana’arsu ta kiwo.

Da yake jawabi yayin horon, shugaban shirin na L-PRES a jihar Farfesa Usman Bello Abubakar, yace manufar shirin shine zamanantar da kiwo don samun gwaggwabar riba da magance rikicin manoma da makiyaya dake addabar ƙasar nan.

Yace “An bar harkokin kiwo a baya ba kamar sauran harkokin noma ba, don haka shirin L-PRES ya yunƙuro don ganin shima kiwo ya samu kulawar data dace don zamanantar da shi da maishe shi sana’a mai ƙayatarwa da riba”.

Shugaban yace sakamakon tallafin da gwamnatin Jihar Gombe ke baiwa shirin, L-PRES ya zo da tsare-tsare da dama na inganta kiwon dabbobi da harkokin da suka jibinci kiwo don samar da ƙarin ayyukan yi, da yaƙi da talauci da kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a Najeriya.

Da yake ƙira ga mahalarta taron su 114 su koyar da sauran makiyaya ilimin da suka karu da shi, Farfesa Usman Bello ya buƙacesu su sanya sabbin dabarun da suka samu a aikace don yauƙaƙa ribarsu a sana’ar kiwo.

Da yake ƙaddamar da horaswar, Kwamishinan Ma’aikatar Noma, Kiwo da Bunkasa Kungiyoyin Gama Kai na jihar Dr Barnabas Malle wanda babban Sakataren Ma’aikatar Dr Ibrahim Yakubu ya wakilta, yace gwamnatin jihar a shirye take ta magance matsalolin manoma da makiyaya ta shirye-shiryen zamani irin su L-PRES.

A nashi jawabin, shugaban ƙungiyar MACBAN na jihar Modibbo Yaya, yace wannan lokacin ne ya fi kowanne dacewa don zamanantar da harkokin kiwon dabbobi musamman ganin yadda makiyaya ke fuskantar kalubale daban-daban a sana’ar tasu.

Ya yabawa gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki bisa samar da shirin, yana mai cewa sanadiyyar shirin na L-PRES, makiyaya da sauran masu kiwo za su ci gajiyar dawainiyar da suka daɗe suna yi a tsawon shekaru.

Da yake jawabi a madadin mahalarta taron, shugaban ƙungiyar Kautal Hore na Jihar Gombe Ardo Chindo Abubakar, ya yabawa shirin na L-PRES, da gwamnatin Jihar Gombe da sauran masu ruwa da tsaki bisa kawowa makiyaya ɗauki a daidai lokacin da sana’arsu ke cikin halin ƙaƙanikayi.

Ya bada tabbacin cewa zasu yi amfani da ilimin da aka samu yayin horon, tare da yaɗa shi ga sauran al’ummomin yankunansu.

A yayin horon, ƙwararren a fannin kiwon dabbobi Mahmud Ibrahim Bello, ya gabatar da maƙala mai taken “Sarrafa Dabarun Kiwon Dabbobi a Jihar Gombe”, inda ya koyar dasu yadda zasu sarrafa da alkinta karmami da ciyawar gonakinsu ya zuwa abincin dabbobi.

A yayin horaswar, mahalarta sun samu damar yin tsokaci, da bada shawarwari da kuma yin tambayoyi kan ababen da suka shige musu duhu tare da samun amsoshi.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • 2027: Coalition Endorses Dr. Suleiman for Bauchi Governorship
  • Obasanjo, Inuwa Commissions Ultramodern Premier Seeds Industry at Muhammadu Buhari Industrial Park
  • JED Management Commiserates With Governor Yahaya Over Tudunwadan Pantami Tragedy
  • Bauchi Allied Conservative Congress Organizes Party’s Stakeholders Meeting
  • Bala Mohammed’s Leadership Model Seen as Symbol of Hope on Democracy Day

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2025 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme