Daga Yunusa Isa, Gombe
A ƙoƙarinsa na magance rikicin manoma da makiyaya a Jihar Gombe, Shirin Zamanantarwa da Bunƙasa Kiwo da ake ƙira L-PRES, ya bada kwangilar Naira miliyan 200 don sake shata burtalolin shanu 37 da gandun kiwo 7 a faɗin ƙananan hukumomin jihar 11.
Da yake jawabi gabanin rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Gombe, Ko-odinetan shirin a jihar Farfesa Usman Bello Abubakar, yace bada kwangilar na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na tabbatar da dauwamammen zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Gombe.
Farfesa U.B Abubakar yace a ƙarƙashin shirin na L-PRES wadda ya ƙuduri aniyar kawo sauyi a ɓangaren kiwo, gwamnatin Inuwa Yahaya ta yi nazari kan daɗaɗɗun burtalolin shanu da gandun kiwon da ake da su waɗanda manoma da al’ummar gari suka yi kutse a cikinsu.
Ko’odinetan na L-PRES yace an bada kwangilar ce don sake fasali da fidda iyakokin burtaloli da gandun kiwon don hana manoma sake yin kutse a cikinsu, da kuma hana makiyaya barnata gonakai.
Ya bayyana kyakkyawar fatan cewa “Da wannan matakin, jiharmu ta buɗe sabon babi na tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da ci gaba a tsakanin manoma da makiyaya. Tabbas wannan zai magance mana samun irin abinda ke faruwa a jihohin Arewa Maso Yamma, lamarin daya zama barazana ga tsaron kasa baki ɗaya.”
Farfesa Bello Abubakar ya yabawa gwamnatin jihar bisa kafa kwamitocin riga-kafin rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda yace sun yi tasiri sosai wajen daƙile rikicin dake faruwa duk shekara tsakanin ɓangarorin biyu.
Ya kuma yi ƙira ga manoma da makiyaya da sarakunan gargajiya su baiwa kamfanin dake kwangilar da ma’aikatansa goyon baya don samun nasarar aikin.
A nasa ɓangaren, Surveyor Ibrahim Saeh wanda ya sanya hannu kan kwangilar a madadin kamfanin I.S. Surveying & Geo Informatics Limited da kuma Ignited Goals Limited da aka baiwa kwangilar, ya tabbatar cewa za su aiwatar da aikin akan lokaci, kuma bisa sharuɗan da aka amince da su.
A saƙonsu na fatan alheri, Shugaban Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na jihar Alhaji Modibbo Yaya da Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) reshen Jihar Gombe Modibbo Sadik Ahmad Nafaɗa da sauran masu ruwa da tsaki, sun yaba da wannan yunƙuri na gwamnatin jihar ta hannun shirin na L-PRES.
Sun kuma bada tabbacin haɗin kai da goyon baya ga aikin, da ƴan kwangila da kuma gwamnatin jihar wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin manoma da makiyayan jihar.
Ana dai sa ran kammala kwangilar ce cikin watanni 6.h