Daga Yunusa Isa, Gombe
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) ta miƙa tallafin kayan noma ga Gwamnatin Jihar Gombe da sanatoci uku na Gombe ta Arewa, Gombe ta Tsakiya da Gombe ta Kudu.
Da yake jawabi yayin miƙa kayayyakin a Gombe, Muƙaddashin Ko-odinetan Hukumar Raya Yankin na Arewa Maso Gabas a Jihar Gombe, Rufa’i Lawan Baba Manu, yace an ɗauki matakin ne don aiwatar da shirin shugaban ƙasa na inganta samar da abinci a Jihar Gombe, Arewa maso gabas da Najeriya baki ɗaya.
Yace “Kamar yadda kuka sani, aniyar mu ne mu bunƙasa noman rani, don haka burinmu shi ne mu haɗa kai da gwamnatin jiha da sauran masu ruwa da tsaki don ganin mun tallafawa manoma kai tsaye ba tare da wani cikas ba.”
Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya za ta yi adalci wajen tabbatar da an yi amfani da kayan aiki da sinadaran yadda ya kamata don samun sakamako mai kyau.
Ya yi ƙira ga manoman da za su amfana su ɗauki wannan tallafi a matsayin wata babbar dama ta bunƙasa sana’arsu, yana mai tabbatar da cewa sun samar da hanyoyin bibiya da sanya ido don tabbatar da cewa ba a karkatar da kayayyakin ba.
Da yake jawabi a madadin gwamnatin jihar, wakilin kwamishinan noma da kiwo na jihar Mista Jonathan Bulus, da Wakilin Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa Hassan S. Dogarai, sun yabawa hukumar ta NEDC bisa wannan tallafi, suna masu tabbatar da cewa matakin zai taimakawa ƙoƙarinsu wajen samar da wadataccen abinci a jihar.
Kwamishinan ya bada tabbacin cewa za a tabbatar kayan aiki da sinadaran noman sun kai ga manoman ainihi a jihar, yana mai cewa matakin zai taimaka matuka wajen inganta manoman rani.
Yace akwai wurare kimanin 46 da ake noman rani bana a faɗin Jihar Gombe.
Bulus ya ƙara da cewa kasancewar Jihar Gombe jihar manoma, wannan tallafi ya zo a lokacin da ya dace musamman ga manoman rani, waɗanda yace za su iya amfani da kayan aikin wajen inganta nomansu na damina idan aka samu fari.
Kayayyakin noma da sinadaran da hukumar ta NEDC ta baiwa gwamnatin jihar sun haɗa da taki na ruwa lita 2000, da urea lita 1000, da maganin feshin ciyawa lita 3000, da kuma injunan ban ruwa guda 500.
A ɗaya ɓangaren kuma, kowanne daga cikin sanatocin jihar uku ya samu taki NPK lita 300, da urea lita 200, da maganin feshin ciyawa lita 700, da injunan ban ruwa guda 100 da kuma tukwanen girki guda 50 don rabawa ga al’ummomin mazaɓunsu.