Daga Yunusa Isa, Gombe
Rundunar ƴan sanda a Jihar Gombe ta yi holen wassu mutane 4 da take zargi da satan ƙarafan jirgin ƙasa guda 42, da wassu mutanen 3 da ake zargi da laifin fyaɗe da kuma wani da ake zargi ɗan garkuwa da mutane ne.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedkwatar rundunar a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Hayatu Usman, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Buhari Abdullahi, yace ‘yan sandan sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da haɗin baki, da haddasa ɓarna da satan ƙarafan jirgin ƙasa da kuma karbar kayan sata.
Yace uku daga cikin waɗanda ake zargin sun kware wajen lalata kadarorin gwamnati, kuma an kama su ne a layin dogo na Liji a Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ɗauke da wasu ƙarafan titin jirgin ƙasa guda 42 a boye a cikin wata farar akori-kura ɗauke da yashi don ɓadda sawu.
Jagoran waɗanda ake zargin Yusuf Mohammed ya amsa laifinsa, yana mai cewa sau bakwai yana yin irin wannar aika-aika.
Yace wani mai suna Shu’aibu Saidu na Unguwa Uku ne ke sayan ƙarafan satan, kuma shi ma ya amsa laifinsa.
Kakakin rundunar yace sun kuma kama wasu mutane uku da ake zargi da laifin fyaɗe, ɗaya daga cikin su mai kimanin shekaru 45 da ake zargi da yi wa wata yarinya fyade sau biyu a gidansa.
Ɗayan wanda ake zargin kuma an kama shi ne da laifin sanyawa wata yarinya yatsa a gabanta a lokacin da ya kai ta wani lungu a anguwar Hammadukaf dake cikin garin Gombe.
Wanda ake zargi da laifin fyaɗen na ƙarshe shine wani yaro ɗan shekaru 13, wanda ake tuhuma da yiwa yarinya ‘yar shekaru takwas fyaɗe bayan daya ja ta zuwa wani lungu a anguwar Batari dake Kumo, inda ya yi mata fyaɗen.
Kakakin ya kuma gabatar da wani da suka kama da ake zargin ɗan garkuwa da mutane ne, wadda aka samu a dajin Zange na Ƙaramar Hukumar Dukku, inda aka same shi yana gadin wata mata da aka sato daga ƙauyen Akkoyel.
Buhari yace rundunar tana nan kan bakanta don tabbatar da an kamo sauran abokan burminsa uku da suka tsere.
Yace nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.
Da yake jaddada ƙudurin rundunar na daƙile aikata laifuka, kakakin ƴan sandan ya yi ƙira ga al’ummar Jihar Gombe su baiwa rundunar hadin kai a kodayaushe tare da baiwa yan sanda bayanai masu muhimmanci game da duk wani motsin da basu gamsu da shi ba.
Ya kuma ankarar da iyaye su riƙa kula da lungunan dake tsakanin gidajensu, yana mai cewa a irin waɗannan wuraren ne masu aikata fyaɗen ke samun mafaka.