Skip to content
Jewel Times
Menu
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Sample Page
Menu

NNPP A Gombe Ta Kalubalanci Shugabanni Kan Sadaukarwa Da Farfado Da Jam’iyya Daga Tushe

Posted on March 22, 2024 by Jtimes

Daga Yunusa Isa, Gombe

Shugaban Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na Gombe Barista Rambi Ibrahim Ayala, ya ƙalubalanci sabin shugabannin jam’iyyar na shiyya da na ƙananan hukumomi su tashi tsaye wajen ganin jam’iyyar ta yi nasara a yankunansu daban-daban.

Rambi ya yi wannan ƙalubale ne yayin taron farko na kwamitin gudanarwan jam’iyyar na jiha a Gombe.

Shugaban ya kuma ƙarfafa gwiwar shuwagabannin shiyya dana ƙananan hukumomi da aka ƙaddamar a yayin taron, su tabbatar da cewa jam’iyyar ta kafu kuma ta yi tasiri a dukkanin mazaɓun sanatoci uku da ƙananan hukumomi 11 na jihar.

“Ba a fara siyasa daga sama, ana fara siyasa ne daga ƙasa, a matsayinmu na shugabanni dole ne mu koma gundumominmu daban-daban, da ƙananan hukumomi, da shiyyoyinmu har zuwa matakin jiha don ƙarfafa jam’iyyarmu ta NNPP abar ƙaunarmu. Wannar ita ce hanya ɗaya tilo da za mu gina jam’iyyar nan har ta yi amo”.

Yace duba da yawan shugabannin jam’iyyar kimanin 3801 daga matakin gunduma zuwa jiha, NNPP ta kafa ƙwaƙƙwaran ginshiƙin da zai kaita ga samun nasara a kowane zaɓe.

Da yake ba da tabbacin samar da ofisoshin jam’iyyar a kowane mataki, Barista Rambi Ayala ya buƙaci shugabannin su lalubo hanyoyin da za su bi wajen bada gudunmawar data dace don samun nasarar jam’iyyar.

A saƙonninsu na fatan alheri, wasu shugabannin jam’iyyar sun yi ƙiran kan haɗin kai, jajircewa, himma da kwazo don ganin NNPP ta samu nasara a zaɓe mai zuwa.

A nasa jawabin, Alhaji Babangida Sakatare ya ja hankalin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar cewa su maida hankali kan ɗaukar sunayen shugabannin dake halartar tarukan jam’iyyar, don bambance jajirtattu daga shugabannin je-ka-na-yi-ka.

Sauran shugabannin kamar su Auwal Muhammad, Musa Alhasan Aliyu Kwarra da Sani Ibrahim Jalo, sun ba da shawara kan matakan da ya kamata a ɗauka don sanya tutocin jam’iyyar a wurare masu muhimmanci na faɗin jihar.

Sun kuma shawarci majalisar gudanarwar jam’iyyar ta jiha ta zayyana ayyukan da suka rataya akan kowane shugaba don magance shiga ayyukan juna.

Suma a nasu jawabin, Andrew Simon da Habiba Adamu Garba, sun ƙarfafa gwiwar jam’iyyar kan ta riƙa tafiya da kowa, tare da shawartar ɗokacin shugabannin su rika sauƙe nauyin dake kansu.

A ɗaya ɓangaren kuma, Ɗahiru Aliyu da Umaru Ali Chilo waɗanda suka buƙaci shuwagabanni da sauran ƴaƴan jam’iyyar su riƙa sadaukar da dukiyarsu don ci gaban jam’iyyar NNPP, sun shawarci majalisar zartaswar jam’iyyar ta jiha ta mutunta tsarin sakantawa waɗanda suka sha wa jam’iyyar wahala.

Mai baiwa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a Barista David Ishiyaku yace idan shugabanni da ƴaƴan jam’iyyar suka sanya himma, ƙwazo da jajircewa, babu abin da zai hana NNPP kafa gwamnati a Jihar Gombe a 2027.

A yayin taron, Barista Ayala ya gabatar da sabbin katunan jam’iyyar ta NNPP da kundin adana bayanai ga shuwagabannin jam’iyyar na shiyya dana ƙananan hukumomi don ci gaba da rajistar sabbin mambobi zuwa cikin jam’iyyar.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • 2027: Coalition Endorses Dr. Suleiman for Bauchi Governorship
  • Obasanjo, Inuwa Commissions Ultramodern Premier Seeds Industry at Muhammadu Buhari Industrial Park
  • JED Management Commiserates With Governor Yahaya Over Tudunwadan Pantami Tragedy
  • Bauchi Allied Conservative Congress Organizes Party’s Stakeholders Meeting
  • Bala Mohammed’s Leadership Model Seen as Symbol of Hope on Democracy Day

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2025 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme