
Gwamnatin Jihar Gombe cikin alhini, ta sanar da rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Kanar Abdullahi Bello (Mai Ritaya) wanda ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi ranar Juma’ar nan kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe.
Wata sanarwar da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya fitar tace “Ya rasu ne tare da ɗan sandan dake tsaronsa, Sajan Adamu Husaini yayin da suke dawowa daga Maiduguri Babban Birnin Jihar Borno, bayan halartar taron tuntuɓa na Yankin Arewa Maso Gabas kan ci gaba da kwance ɗamarar makamai da sauya tunanin yan ta’adda (DDR)”.
Misilli yace Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya samu wannan labari mai ratsa zuciya cikin baƙin ciki mai tsanani, inda ya bayyana marigayi Kwamishinan a matsayin jami’i mai ɗa’a kuma mai himma da ƙwazo akan aikin gwamnati, wanda ya yi amfani da ɗimbin ƙwarewarsa ta aikin soja da jagoranci da kishin ƙasa wajen ci gaban Jihar Gombe, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron da jihar ta yi suna da su.
“Za a riƙa tunawa da Col. Abdullahi Bello (Mai Ritaya) a matsayin ginshiƙi wajen tabbatar da ɗa’a, jajircewa da sadaukar da kai, yayinda ya gudanar da ayyukansa cikin himma da sanin ya kamata. Rasuwarsa babban rashi ne ba ga iyalansa da gwamnatinmu kaɗai ba, har ma ga Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya,” in ji Gwamna Inuwa Yahaya.
Ya tuno irin gudunmawar da marigayin ya bayar a Majalisar Zartarwa ta Jiha, musamman wajen tsara manufofin tsaron cikin gida, da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kare lafiyar al’umma.
Gwamna Inuwa Yahaya, a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da ‘yan uwansa, da al’ummar Ƙaramar Hukumar Balanga, inda ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma saka masa da Aljannar Firdaus.
Hakazalika Gwamnan ya jajantawa iyalan marigayi dogarin ɗan sandan, Sajan Adamu Hussaini wanda shi ma ya rasa ransa a wannan mummunan hatsari, yana mai bayyana mutanen biyu a matsayin ’yan kishin ƙasa waɗanda suka mutu a hidimar jiha da ƙasa baki ɗaya. Ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa direban Kwamishinan lafiya da gaggawa, wanda a halin yanzu yake samun kulawa sakamakon raunukan da ya samu a hatsarin.
