Daga Yunusa Isa, Gombe

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hatsura ta Ƙasa Reshen Jihar Gombe Samson Kaura, ya karrama jami’an hukumar 10 da suka samu ci gaba a aiki, bayan da sun canza sheƙa daga rukunin dakaru zuwa jami’ai.

 

Da yake jawabi a yayin bikin a hedkwatar hukumar dake Lafiyawo, kwamandan yace sauya sheƙar ya biyo bayan nasarar da jami’an suka samu ne na ƙaro karatu, wanda hakan ya sa suka samu manyan takardun shaida daga manyan makarantu da jami’o’i daban-daban.

Da yake jan hankalin sauran dakaru da jami’an hukumar kan su yi amfani da damar da suke da ita wajen karo ilimi don samun ci gaba a hukumar, Kwamanda Kaura ya buƙaci sabbin jami’an su sadaukar da kansu wajen ƙara kare rayuka da dukiyoyin masu amfani da hanyoyi.

 

Kwamandan ya ƙara da cewa, “Wanda aka yiwa goma ta arziƙi ya kamata ya ramawa kura aniyarta. Wannan sauyi da kuka samu tamkar ƙira ne na ganin kun ƙara sadaukar da kai ga aikin”.

Yace jami’an da abin ya shafa sun hada da Superintendent Route Commander mutum 1, da Route Commander 1, Deputy Route Commanders 4 da kuma Assistant Route Commanders mutum 3.

 

Da yake taya sabbin jami’an murna, Kaura ya buƙaci su jajirce don sauƙe sabbin nauyin dake tattare da sabon ci gaban da suka samu.

Yace hukumar ta bullo da sabbin matakai a gangaminta na watannin ƙarshen shekara na bana don ƙara rage aukuwar hatsurra ta hanyar wayar da kan fasinjoji da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Yayin da yake yabawa ƙoƙarin masu ruwa da tsaki daban-daban wajen rage hatsura a kan hanyoyi, kwamandan hukumar kiyaye hatsuran ya bada tabbacin cewa jami’an rundunar maza da mata a tsaye suke don tabbatar da an samu raguwar hatsura a watannin na ƙarshen shekara, da lokutan bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara.

Da take jawabi a madadin sabbin jami’an da aka karraman, Altine Ahmed ta yabawa shugaban hukumar kiyaye hatsdura na ƙasa Shehu Muhammad bisa amincewa da sauya musu sheƙan, tana mai yabawa kwamandan rundunar na Jihar Gombe Samson Kaura bisa goyon baya da jagorancin da ya yi musu a tsawon wannan lokaci.

 

Ta bukaci karin tallafi da goyon baya daga manyan jami’an hukumar don ba su damar sauƙe sabon nauyin da aka ɗora musu cikin nasara.

Da take ba da tabbacin jajircewarsu wajen gudanar da sabbin ayyukan nasu cikin himma, Altine ta buƙaci sabbin jami’an su dage tare da sadaukar da kai wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyoyi.

 

Iyalai da ‘yan uwa da abokan arziƙi da dama ne suka halarci taron cike da farin ciki da taya yan uwansu murna.