Daga Yunusa Isa, Gombe
Don alamta kawo ƙarshen makon tunawa da waɗanda hatsura suka rutsa da su na 2024, Ƙungiyar Matan Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsura ta Kasa (ROSOWA) Reshen Jihar Gombe, ta tallafa tare da yin addu’o’i ga waɗanda hatsura suka rutsa da su da sauran marassa lafiya a asibitin ƙwararru na Jihar Gombe.
Da take zantawa da manema labarai yayin ziyarar, shugabar ƙungiyar ta ROSOWA a jihar Madam Rahila Apaji, tace “Mun yi wannan tallafin ne don tausayawa da karfafawa da kuma yin addu’o’i ga waɗanda hatsura suka rutsa da su da sauran marasa lafiya a wani ɓangare na bukukuwan makon tunawa da waɗanda hatsura suka rutsa da su na 2024”.
Shugabar ta jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a hatsura, inda ta yi addu’ar Allah Ta’ala ya gafarta musu ya kuma ba su kwarin guiwar jure rashinsu.
Ta yaba da irin kyakkyawar tarbar da mahukuntan asibitin kwararru na jihar suka yi wa tawagar, inda ta bada tabbacin cewa ROSOWA zata ci gaba da wannan ƙoƙari har ma da faɗaɗa shi.
A nasa jawabin, Ko-odinetantan jami’ai na musamman na hukumar ta FRSC a jihar Mr Moses Obi Nnadi, yace ana samun ƙaruwar hatsura a watannin ƙarshen shekara, don haka hukumar take ƙara ƙoƙari wajen rage aukuwar hatsura.
A nasa jawabin, babban Daraktan asibitin kwararru na Jihar Gombe Dr Mu’azu Shu’aib wanda Shugaban Ma’aikatan Jinya na asibitin Danladi Gambo ya wakilta, ya yabawa ƙungiyar ta ROSOWA bisa irin tallafin da ta saba baiwa marasa lafiya, inda ya yi addu’ar Allah ya saka mata da mafificin alkhairi.
Yayin da yake ƙarfafawa ƙungiyar matan gwiwa kan su ci gaba da wannan karimci, daraktan ya buƙaci sauran ƙungiyoyi su yi koyi da ROSOWA.
A jawabinsa na godiya a madadin majinyatan da suka amfana da tallafin, Baba Ahmad Tugga, ya bayyana matuƙar godiyarsu ga ƙungiyar ta ROSOWA yana mai addu’ar Allah Ta’ala ya saka mata da alkhairi.
“A gaskiya mun ji daɗin kulawa da nuna ƙaunarku a gare mu, yadda kuka zo musamman don duba mu kuma har ma da ɗan tallafi. Wannan yana nuni da cewa akwai wassu mutane a waje dake tunawa da mu har ma da tausaya mana. Muna godiya, Allah ya saka da alheri.” .
Tawagar ta gudanar da addu’o’i na musamman kan Allah ya baiwa waɗanda suka jikkata ko suke fama da jinya lafiya.