Daga Yunusa Isa, Gombe
Gwamnatin Jihar Gombe ta karɓi farashin kamfanoni biyar dake neman kwangilar gina hanyoyi masu tsawon kilomita 1.2 a Kwalejin Jinya da Ungozoma ta Jihar.
Da yake jawabi yayin karɓar farashin, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Injiniya Usman Maijama’a Kallamu, ya baiwa kamfanonin tabbacin yin adalci wajen tantance buƙatun da suka gabatar.
Yace “Biyo bayan gina kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta zamani da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi, Gwamnan ya ga ya dace a ba da kwangilar gina tituna don haɗe ɓangarori daban-daban na kwalejin da hanyoyin na zamani”.
Da yake yabawa kamfanonin kwangilan kan yadda suke gudanar da ayyuka masu inganci a jihar, Maijama’a Kallamu ya buƙaci kamfanonin su riƙa kammala ayyukansu a kan lokaci don samun damar fara wassu.
Kwamishinan ya bada tabbacin kammala ayyukan hanyoyin kafin damina ta kankama. Ya kuma bukaci al’ummar jihar su riƙa addu’a tare da marawa gwamnatin Inuwa baya don samun ƙarin ribar demokradiyya.
A saƙonninsu na fatan alheri, Shugaban Ƙungiyar Injiniyoyi ta Najeriya Reshen Jihar Gombe Injiniya Hamzat Abubakar, da Ko’odinetan shiyya na Conren Injiniya Jonathan Mshelia, da kuma wakilin ’yan kwangila QS Pakison, sun yaba da tsarin neman kwangilar wadda suka ce an yi shi a fayyace.
Suka ce ƴan kwangila uwa ɗaya uba ɗaya suke, don haka duk kamfanin da ya samu nasarar samun kwangilar nasararsu ce baki ɗaya.
Tun farko a jawabinsa wakilin Babban Daraktan Ofishin Tabbatar da Bin Ƙa’idoji a Harkokin Gwamnati Injiniya Gideon Mele, yace kamfanonin da suka gabatar da farashin nasu sun haɗa da Kamfanin Grandscope Construction Limited wadda yace zai yi hanyar akan Naira biliyan 1 da miliyan 900 tare da kammalawa cikin watanni huɗu.
Sai Kamfanin EEC International Limited wadda yace zai yi aikin akan Naira biliyan 2 da miliyan 410 tare da kammalawa a watanni bakwai. Sai Kamfanin Triacter Nigeria Limited da ya yi tayin yin aikin a Naira biliyan 1 da miliyan 160 tare kammala aikin cikin watanni uku, yayin da kamfanin Tinka Point Nigeria Limited ya miƙa tayin yin aikin akan Naira biliyan 2 da miliyan 200 tare da kammala aikin a watanni biyar.
Injiniya Mele ya buƙaci ’yan kwangilan su bi ƙa’idojin kwangila tare da yin aiki mai inganci da kuma kammala shi akan lokaci.
Ya kuma yi ƙira ga jami’an sanya ido kan ayyuka su riƙa bibiyar ayyukan yan kwangila don tabbatar da ana yinsu da inganci.