Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya Kwamared Alhassan Yahya Abdullahi murnar zaɓensa da aka yi a matsayin Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa (NUJ).

 

Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga Jewel Times Hausa.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matuƙar farin cikinsa bisa gagarumar nasarar da Alhassan ya samu a wajen taron ƙungiyar karo na 8 da aka kammala a garin Owerri na Jihar Imo, inda ya bayyana hakan a matsayin wani gagarumin nasara kuma abin alfahari ga jihar da ɗokacin ƴan jarida.

Gwamnan ya yaba da salon Kwamared Alhassan da gagarumin ci gaban da ya cimma a shugabancin NUJ.

 

“Tun daga inda ka fara a matakin ƙungiyar yan jarida zuwa matakin jiha, shiyya da ƙasa baki ɗaya, ka nuna jajircewa da riƙon amana da kishin aikin jarida da kyautata jin daɗi da walwalar ƴan jarida.

 

Zaɓenka da ka yi a matsayin shugaban NUJ na ƙasa, ya nuna irin amincin da ‘yan jarida ke da shi kan shugabancinka a faɗin Nijeriya. Jajircewa, aminci da hangen nesanka sun sanya ka zama kyakkyawan misalin abin da ake nufi da zama jagora a fagen aikin jarida,” in ji Gwamnan.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatarwa Kwamared Alhassan goyon baya, haɗin kai da fatan alherin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe a yayin da zai fara wannan muhimmin aiki, inda ya bayyana ƙwarin guiwarsa wajen samun haɗin kai a jagorancin ƙungiyar ta NUJ wajen samun ƙwarewa da ci gaba.

 

“Yayin da ka fara wannan gagarumin aiki, muna baka tabbacin cewa Jihar Gombe za ta tsaya tsayin daka don mara maka baya, muna da yaƙinin cewa a ƙarƙashin jagorancinka, ƙungiyar NUJ za ta samu sabon zamani na ci gaba, haɗin kai, da sanin makamar aiki wanda zai ƙara ɗaukaka matsayin aikin jarida da inganta ci gaban ƙasa.

 

Nasarar da ka samu ba nasara ce kawai ga NUJ ba, alama ce ta kyawawan halayenka na jagoranci, jajircewa, da nagarta,” in ji shi.

 

Gwamna Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Jihohin Arewa, ya bayyana cewa zaɓen Alhassan a matsayin shugaban NUJ na ƙasa ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar jagoranci mai ƙarfi da hangen nesa don haɗa kai da kuma ciyar da harkar yaɗa labarai gaba wajen tinkarar al’amuran ƙasa da ƙalubalen ci gaba.

 

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwarewar Kwamared Alhassan, ya sanya shi a matsayin wani jigon haɗin kai da tattaunawa don zaburar da ci gaba, ba kawai a ƙungiyar NUJ ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.

 

Da yake yabawa ‘yan jarida bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, Gwamnan ya yi addu’o’i da fatan alheri ga sabin shugabannin ƙungiyar ta NUJ, tare da bayyana muhimmiyar rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen tabbatar da haɗin kai da sadaukarwa wajen ciyar da demokraɗiyya da ƙasa gaba.