Gwamnatin Jihar Gombe ta ɓullo da aikin tsabtace muhalli na gama gari don tabbatar da tsabar muhalli da kyautata lafiyar al’ummar Jihar Gombe.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da amincewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wacce Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Ismaila Uba Misilli ya miƙawa Jewel Times Hausa, yana mai cewa an ware duk ranar Asabar ɗin ƙarshe na kowane wata a matsayin ranar tsaftar muhalli a faɗin jihar, farawa daga wannan wata.
Takardar mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan Ruwa, Muhalli da Gandun Daji Mohammed Sa’idu Fawu, ta bayyana cewa za a riƙa gudanar da aikin tsabtace muhallin ne daga ƙarfe 8:00 zuwa 10:00 na safe, kuma za a aiwatar da dokar taƙaita zirga-zirgar jama’a da ababen hawa, sai dai ga mutanen dake aiwatar da muhimman ayyuka.
A wani ɓangare na takardar ta yi bayanin cewa, “A bisa ƙudurin wannar gwamnati na inganta muhalli da kyautata lafiyar jama’a, Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya CON, (Ɗan Majen Gombe), ya amince da gudanar da ayyukan tsabtar muhalli a duk wata. Aikin tsaftar muhallin a jihar wadda jama’a za su gudanar a duk ranar Asabar ta ƙarshen kowane wata”.
“Don haka, za a taƙaita zirga-zirga a daidai wannan lokacin (sai dai waɗanda suke gudanar da muhimman ayyuka). Haka kuma, ana umurtar dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sauran jama’a su bi umarnin, domin tawagar jami’an ma’aikatar ruwa. Muhalli da Gandun daji da kuma Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar Gombe (GOSEPA) za su sanya ido sosai don tabbatar da bin wannan umarni,” in ji sanarwar.