
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da naɗin sabbin shugabanni da mambobi a wassu manyan kwamitoci da hukumomin Jihar Gombe.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi, wanda ya sanar da amincewar gwamnan, yace naɗe-naɗen na da nasaba da ci gaba da jajircewar gwamnatin jihar na ƙarfafa cibiyoyi da hukumomi don inganta shugabanci na gari.
Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga Jewel Times Hausa yau Laraba.
Hukumar Kula da Ma’aikata:
Sabbin shugabannin da aka naɗa a hukumar kula da ma’aikata ta Jihar Gombe sune:
1. Madam Rabi Shuaibu Jimeta – Shugaba
2. Malam Masoyi Bilwa Sajo – Babban Kwamishina
Adamu S. Musa – Babban Kwamishina
Dr. Garba Muhammed Bajoga – Babban Kwamishina
Hon. Adamu Jani Bello – Babban Kwamishina
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC):
Ita ma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, wadda aka ɗorawa alhakin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi, an sake naɗa mata shugabanni kamar haka:
Alhaji Abdullahi Garba Talasse – shugaba
Maisamari Enos Dulle Kushi – Babban Kwamishina
Dr. Abubakar Abdullahi Kumo – Babban Kwamishina
Ahmed Abba Abubakar – Babban Kwamishina
Hon. Ado Umar – Babban Kwamishina
Yusuf Ishaq Baji – Babban Kwamishina
Hon. Abubakar Kunuwal – Babban Kwamishina
Mohammed Hussani Muhammad – Babban Kwamishina
Hukumar Kula da Malamai:
Don ƙarfafa fannin ilimi, an naɗa mutane kamar haka don jagorantar Hukumar Kula da Malamai:
Musa Aliyu Hinna (Marafa) – Babban Mamba
Mohammed Kabiru Abdullahi (Kwami) – Babban Mamba
Aminu Musa (Coach) – Babban Mamba
Hamid Alhaji Mohammed – Mamba na wucin gadi
Bashir Santuraki Dukku – Mamba na wucin gadi
Mr. Sunday Zailani – Mamba na wucin gadi
Ƙafar Yaɗa Labarai ta Jihar Gombe (GMC):
A wani yunƙuri na sauya fasalin kafafen yaɗa labarai na jihar, an yi wa hukumar yaɗa labaru ta Jihar Gombe garambawul da muƙamai kamar haka:
Barr. Abdullahi Jalo (Castic) – Shugaba Ibrahim Isa – Babban Darakta kuma Mamba
Engr. Adam Hassan Musa (Bimason) – Mamba
Nasiru Adamu El-Hikaya – Mamba
Abdulbasid Moh’d Inuwa – Mamba
Mrs. Habiba Jonathan – Mamba
Ibrahim Jabiru Kuri – Mamba
Umar Aliyu Shamaki – Mamba
Miss. Tabitha Iliya – Mamba
Yakubu Ibn Mohammed – Mamba
Salisu Ibrahim Nagodi – Mamba
Wakilin Ma’aikatar Kuɗi – Mamba
Wakilin Ma’aikatar Watsa Labarai – Mamba
Mashawarcin Shari’a, GMC – Sakatare
Hukumar Gudanarwar Kwalejin Jinya da Ungozoma:
Haka kuma an naɗa Dr. Babangida Hammani a matsayin mamban cike gurbi a kwamitin gudanarwar jinya da ungozoma na Jihar Gombe.
A cewar Sakataren gwamnatin yace duk naɗe-naɗen sun fara aiki ne daga yau Laraba 9/07/2025.
Misilli yace “Gwamna Inuwa Yahaya yana sa ran sabbin waɗanda aka naɗan za su riƙe amanar jama’a tare da yin aiki cikin himma da riƙon amana da sadaukarwa don ci gaban Jihar Gombe”.
