Skip to content
Jewel Times
Menu
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Privacy Policy
  • Sample Page
  • Terms and Conditions
Menu

Gwamna Inuwa Ya Nada Ibrahim Isa Na BBC A Matsayin Shugaban GMC

Posted on February 12, 2024 by Jtimes

… Kana Ya Ɗaga Darajar Dr. Ishiyaku Babayo Daga Babban Mataimaki Na Musamman (SSA) Zuwa Mai Ba Da Shawara Na Musamman Kan Abokan Hulɗan Ci Gaba

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da naɗin Ibrahim Isa na Gidan Rediyon BBC a matsayin Babban Daraktan Kafar Yaɗa Labarai ta Jihar Gombe (GMC).

Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga Jewel Times Hausa yau Litinin.

Misilli yace Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ne ya sanar da amincewar gwamnan, yana mai cewa naɗin na Ibrahim Isa, wadda ya fara aiki nan take, ya samo asali ne daga nagartattun halaye da kwarewarsa a fannin yaɗa labarai.

Ibrahim Isa, yana da ƙwarewar aikin jarida ta fiye da shekaru ashirin, hakan yasa ya yi fice a matsayin ɗan jarida mai tura rahotanni, mai haɗa labaru da karanta su, kuma mai gudanar da shirye-shiryen talabijin kana manajan watsa labarai. Duba da gogewa da kwarewarsa, ana sa ran Ibrahim Isa zai yi amfani da sabbin dabaru da hikimomi a Hukumar Yaɗa Labarun ta Jihar Gombe don inganta harkokin yaɗa labarai.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa jagorancin Ibrahim Isa zai taimaka wajen bunƙasar ƙafar yaɗa labaran ta GMC da yi wa al’umma hidima ta hanyar samar musu sahihan labarai da suka dace.

Har ila yau, Gwamna Inuwa Yahayan ya amince da ɗaga darajar Dakta Ishiyaku Babayo Mohammed, daga matsayin babban mataimaki na musamman (SSA) kan haɗin gwiwa da abokan huldar ci gaba zuwa mai ba da shawara na musamman kan wannan fanni.

Sanarwar hakan wacce Sakataren Gwamnatin Jihar ya sanar, ta ce an ɗauki matakin ne duba da irin nasarorin da Dr. Mohammed ya cimma, da jajircewarsa na musamman da kuma tasirin da ya yi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci daga naɗa shi a matsayin mai bada shawarar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa daga darajarsa zuwa muƙamin mai ba da shawara na musamman zai ƙara haɓaka shirye-shiryen haɗin-gwiwa na jihar tare da ƙara ƙaimi wajen samar da kuɗaɗe da tallafi daga ɓangarori daban-daban na ci gaba don ba da gudummawa ga jin dadi da ci gaban Jihar Gombe baki ɗaya.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • CISLAC Advocates Higher Taxes on Tobacco Products to Discourage Consumption
  • National Cash Transfer Programme Reaches 16,497 Households in Bauchi LGA
  • Gombe RUWASSA Upskills 45 Officers to Bolster Water and Sanitation Infrastructure
  • Revolutionizing Yields: UBRBDA, Cosmopolitan University Empower Gombe Farmers with Climate-Smart Techniques
  • Gombe PDP Dismisses APC Claims, Insists Pantami Has Left the Party

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Human Capital Development
  • Infrastructure
  • Law
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme