Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dr Abubakar Shehu Abubakar na 3 a bikin ‘Hawan Gidan Gwamnati.
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar ta Gombe Ismaila Uba Misilli, yace “Bikin Hawan Sallah na Gidan Gwamnatin da ake yi duk shekara, al’ada ce da aka daɗe ana yi, inda Sarki ke jagorantar hakimai da ‘yan majalisar masarauta waɗanda suka caaɓa ado da kayayyakin sarauta kala-kala, lamarin dake ƙayatarwa, tare da jawo hankalin dubban ‘yan kallo daga sassan jihar daban-daban”.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Inuwa yace gwamnatinsa za ta ci gaba da bada fifiko kan ayyukan da za su ƙara haɓaka tattalin arziki, da samar da ci gaba, tare da bunƙasa jin daɗi da walwalar al’ummar Gombe.
Ya yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya baiwa al’ummar Musulmi damar azumtar watan mai alfarma na Ramadana, wadda hawa idin ƙaramar Sallah da aka yi ranar Laraba ya alamta karshen azumin.
Ya buƙaci Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba a Jihar su ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali wadda Musulunci da Kiristanci suka koyar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da neman goyon baya, haɗin kai, da shawarwari na hikima daga sarakuna iyayen ƙasa da sauran shugabanni don samar da kyakkyawan shugabanci ga jihar.
Gwamna Inuwa ya ci gaba da cewa, duk da ƙalubalen da jihar ke fama da shi ta fuskar kuɗi, gwamnatinsa ta samu nasara a dukkanin ɓangarorin ci gaba, inda ya nuna cewa ingantaccen shugabanci da gyare-gyaren da ake yi ya sa Jihar Gombe ta samu nasarori da dama, musamman ma matsayi mafi armashin data samu na AAA a baya-bayan nan kan ma’aunin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya.
“Na yi farin cikin karɓar baƙuncin Mai Martaba Sarki da ‘yan tawagarsa a wannan bikin na Sallah a gidan gwamnati, a madadina da ɗokacin jami’an gwamnati na, muna maraba da ku sosai,” in ji shi.
Gwamnan ya ƙara da cewa “A duk lokacin da na samu damar yin jawabi ga jama’armu kai tsaye, na kan jaddada ƙudurin gwamnatinmu na haɓaka tattalin arziƙin jihar, muna ba da fifiko kan shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziƙi, ci gaba, da kuma walwalar jama’a, duk da ƙarancin kason da muke samu, muna alfahari ganin yadda Gombe ta zama kan gaba wajen bunƙasar tattalin arziki da ci gaba, godiya ta tabbata ga Allah”.
Ya ƙara da cewa “Matsayin da Jihar Gombe ta samu a fannin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar jama’a a kwanakin baya ya nuna irin jajircewarmu wajen ciyar da jihar gaba, dole ne in jaddada cewa waɗannan nasarorin ba an same su ba ne kawai, sai da jajircewa da gudummawar zaman lafiya da tsaro da kuma goyon bayan al’ummar Jihar Gombe”.
“Ina yabawa sarakunanmu, musamman Mai Martaba Sarkin Gombe, bisa namijin ƙoƙarin da suke yi da haɗin kai da suke bayarwa wajen ganin an cimma waɗannan nasarori.”
Gwamnan ya kuma yabawa masarautun jihar bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu daban-daban dama jihar baki ɗaya.
Tun farko a nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Gombe Dakta Abubakar Shehu Abubakar na 3 yace ya jagoranci hakimai da ‘yan majalisa da masu riƙe da sarautun gargajiya na masarautar ce zuwa gidan gwamnati don taya Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya murna, tare da miƙawa al’ummar jihar gaisuwar masarautar Gombe ta hannun gwamnan, bisa nasarar kammala azumin watan Ramadan, tare da taya shi murnar zagayowar ƙaramar Sallah.
Sarkin ya jinjinawa gwamnan bisa yadda yake tinkarar ɗimbin ƙalubalen da jihar ke fama da su, da kuma yadda yake gudanar da mulkinsa cikin gaskiya wanda a cewarsa ya kai ga aiwatar da wasu ayyuka da zasu sauya rayuwar al’ummar jihar, kamar kafa sansanin masana’antu na Muhammadu Buhari na biliyoyin Naira.
Yace sansanin wani aiki ne na Mahadi-ka-ture, wanda Gombe da al’ummarta za su ci gaba da cin gajiyarsa har tsawon shekaru aru-aru masu zuwa.
“Mai girma gwamna dole in jaddada cewa muna matuƙar alfahari da kai da irin nasarorin da gwamnatinka ta samu cikin shekaru biyar na jagorancinka. Ayyukanka masu kawo sauyi da shirye-shiryenka a bayyane suke gare mu. Ka ɗora Gombe bisa turbar ci gaba mai ɗorewa. A ƙarkashin jagorancinka Gombe tana tashe, kuma tattalin arzikinmu yana bunƙasa. Sansanin masana’antu na Muhammadu Buhari wani dauwamammen gado ne da gwamnatinka ta samar, kuma hakan zai jawo masu zuba jari, da samar da guraben ayyukan yi ga jama’armu, da kuma rage zaman kashe wando.” Inji Sarkin.
Ya kuma jinjinawa gwamnan bisa ƙoƙarinsa a fannonin lafiya da ilimi, musamman gina makarantar zamani ta Kumbiya Kumbiya, da samar da makarantun zamani na musamman guda biyar a faɗin jihar, da kwashe dubban yaran da basa zuwa makaranta tare da mayar da su azuzuwa.
Ya yabawa Gwamnan Jihar ta Gombe kan biyan albashin ma’aikata akan kari da kuma biyan bashin kuɗaɗen gratuti ga ma’aikatan da suka yi ritaya da dai sauransu, inda ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a yanzu a matsayin manyan nasarorin da ba a taɓa ganin irinsu ba a jihar sai a zamanin gwamnatin Gwamna Yahaya.
Yace babu wani fannin da bai shaida irin ci gaban da gwamnatin Inuwa Yahaya ta samar a fadin jihar ba.
Mai Martaba Sarkin Gombe ya buƙaci al’ummar Jihar Gombe su ci gaba da zama lafiya, tare da baiwa gwamnati da masarautu haɗin kai da goyon baya don tabbatar da ingantacciyar zaman lafiya da tsaro a jihar, yana mai cewa duk waɗannan ci gaba da jihar ta samu, sun samu ne albarkacin zaman lafiya da ake mora a jihar.
Daga bisani Sarkin ya jagoranci dubunnan mahaya dawakai sanye da manyan kayan alfarma kala-kala waɗanda suka gudanar da wata ƙayatacciyar hawan daabaa ta burgewa ga gwamnan da sauran manyan baƙi da suka halarci bikin.
Daga cikin muhimman ababen da suka wakana a wurin bikin sun haɗa da miƙa Goron Sallah da gwamnan ya yi ga sarkin don nuna godiya ga ziyarar.