…Tare Da Raba Babura 250 Ga Wassu Ƴan Jam’iyya Da Hakimai Da Dagatan Ƙaramar Hukumar Akko
Daga Yunusa Isa, Gombe
Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai ta 10 kuma ɗan Majalisan Tarayya Mai Wakiltar Mazaɓar Akko Usman Bello Kumo, ya baiwa masu ƙananan sana’o’i fiye da 750 tallafin Naira dubu dari bibbiyu, tare da raba babura fiye da 250 ga ɗokacin hakimai da dagatan Akko da wassu jami’an jam’iyyar da dai sauransu.
Da yake jawabi gabanin rabon kayayyakin a fadojin masu martaba Lamiɗo Akko, da Sarkin Pindiga da kuma Lamiɗo Gona, ɗan majalisan yace tallafin na daga cikin ayyukan mazaɓarsa da ya sanya a kasafin kuɗin 2024.
Usman Bello Kumo yace tallafin kuɗin wadda ya kai jimillar Naira miliyan 150, ya yi shi ne don ƙarfafa ƙananan ‘yan kasuwa maza da mata don tinkarar ƙalubalen tattalin arziƙi da ake fuskanta a halin yanzu.
Ɗan majalisan yace tallafin zai ƙarfafa jarin ‘yan kasuwa da bunƙasa kasuwancinsu.
Da yake tsokaci kan babura 250 ɗin da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 200, ɗan majalisan yace ya yi hakan ne don ƙarfafa gwiwar hakimai da dagatan su tabbatar da tsaro a yankunansu, da kuma kai rahoton duk wata matsalar gaggawa ga na gaba don ɗaukar matakan gaggawa.
Babban mai tsawatarwan yace a matsayinsa na wakilin jama’a, ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen yi musu ingantaccen wakilci ta hanyar samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar mazaɓarsa, da kuma isar da buƙatu da koke-kokensu ga gwamnatin tarayya.
Ya kuma yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa samar da kyakkyawar dama ga ‘yan siyasa a jihar don su samar da ribar demokraɗiyya ga al’ummarsu.
Ya ƙara da cewa nan bada daɗewa ba za a fara aikin sake gina Makarantar Sakandaren Gwamnati ta GDSS Akkoyel Kumo wacce zata laƙume kuɗi Naira Biliyan 1 da miliyan 400.
A saƙonsu na fatan alheri dana maraba a fadojin uku, ‘yan majalisan jiha Hon. Musa Muhammad Wuro Biriji na Akko ta Arewa, da Hon. Abdullahi Abubakar Maiwanka na Akko ta Yamma, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abubakar Muhammad Luggerewo da Shugaban Ƙaramar Hukumar Akko Muhammad Danladi Adamu sun yabawa babban mai tsawatarwan bisa yadda yake ƙaunar al’ummarsa, suna masu bayyana cewa ba a taba yin ɗan majalisa irinsa ba a mazaɓar.
Sun yi ƙira ga sauran wakilai da masu riƙe da muƙaman siyasa su yi koyi da Usman Bello Kumo.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Cibiyar kula da ayyuka ta ƙasa Bappah Babba Ɗan Agundi wanda mataimakinsa Alhaji Nasiru Usman ya wakilta, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda aka aiwatar da tallafin.
Ya buƙaci waɗanda suka amfana da kuɗaɗen su sarrafa su ta hanyar da ta dace.
Suma da suke jawabi, masu martaba Lamiɗo Akko Alhaji Umar Muhammad Atiku, da Sarkin Pindiga Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad da Lamiɗo Gona Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam sun yabawa babban mai tsawatarwan bisa kyakkyawan wakilcin da yake yiwa al’ummar Akko, suna masu ƙarfafa shi kan ya ci gaba da irin wannan wakilci. Iyayen ƙasan sun buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin su yi amfani da kuɗi da baburan yadda ya kamata.