Daga Abubakar Rabilu, Gombe

Wata ƙungiyar matasa dake fafutukar kawo sauyi a Jihar Gombe mai suna ‘North East Coalition of Youth for Progressive Governance and Sustainable Development’ ta bayyana cewa a 2027 Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne zai gaji kujerar Inuwa.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin Gidion Musa, wadda ya ce ƙungiyar tana kira ga tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin arziki Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami da ya amsa ƙiransu a 2027 wajen fitowa takarar gwamana a jihar, yana mai cewa shi yafi cancantar ya gaji kujerar daga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.

Gideon Musa, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da suka ƙira a Gombe suna masu ƙira ga Pantami da cewa ya amsa ƙiransu.

Yace sun amincewa tsohon ministan ne sakamakon ɗimbin nasarorin da ya samu a lokacin da ya zama darakta a Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) da kuma lokacin da yake ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani.

A cewar ƙungiyar, Pantami ya samarwa al’ummar Jihar Gombe damar amfana da fasahar zamani ta hanyar buɗe cibiyoyin fasahar sadarwar zamani (ICT) a makarantu da sassa daban-daban na jihar inda ake horar da jama’a tare da ba su damar shiga yanar gizo kyauta.

“Farfesa Pantami ne ya jagoranci samar da ofisoshi a faɗin ƙasar nan ciki har da nan Jihar Gombe, tsohon ministan ya samar da ci gaba da damammakin ayyukan fasaha a yankin arewa maso gabas”.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa “Waɗannan ofisoshin ba kawai sun inganta haɗin guiwa ba ne, sun ma taimakawa ma’aikatan jihar wajen samun ƙarin dama don haɗin guiwa da dandalin ƙirƙiro da musayar bayanai.”, in ji shi.

Ta buƙaci tsohon ministan ya amince da kiran da ta yi masa na tsayawa takaran gwamnan Jihar ta Gombe a zaɓe mai zuwa na shekarar 2027 sannan suka buƙaci Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya mara masa baya a matsayin wanda zai gaje shi.