Daga Yunusa Isa, Gombe

 

Gamayyar ƙungiyoyin farar hula 15 a Jihar Gombe sun janye Ƙudurinsa na shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

 

Gamayyar ƙungiyoyin ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ƙarshen taron da suka yi mai taken “Bita kan tsaro da zanga-zangar da aka tsara yi a faɗin ƙasar”.

Da yake zantawa da manema labarai a yayin taron, jagoran gamayyar ƙungiyoyin Dr Habeeb Muhammad, yace “Bayan gudanar da taruka da tuntuɓar juna da shugabannin addini, da sarakuna, da ƙungiyoyi, da ɗaiɗaikun jama’a da hukumomin tsaro, mun yanke shawarar janyewa daga zanga-zangar da aka tsara yi a faɗin ƙasar nan”.

 

Dokta Habeeb yace “Wassu dalilan da suka ƙara gamsar da mu mu janyewa daga zanga-zangar, sun haɗa da rashin sanin shugabannin dake jagorantar zanga-zangar, da kuma yiwuwar sauya akalarta ya zuwa tarzoma don haddasa matsalar tsaro”.

Sai dai don hana afkuwar zanga-zangar da aka shirya yi, ƙungiyoyin sun shawarci gwamnati ta ɗauki kwararan matakan magance matsalar rashin tsaro, da wahalhalun rayuwa da ake fama da su, da farfaɗo da matatun mai, da dawo da tallafin man fetur dana wutar lantarki, da rage kuɗaɗen makaranta a manyan makarantu, da rage yawan kudaden da ake kashewa kan gudanar da gwamnati, da rage haraji da kaso 50 cikin ɗari, da kuma aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi yadda ya kamata.

Gamayyar ta yi watsi da zargin da ake yi na cewa gwamnati ce ke ɗaukar nauyinta don sukurkutar da zanga-zangar, tana mai tabbatar da cewa lafiya da tsaro da jin daɗin jama’a su ne manyan abubuwan da suka fi damuwa da su.

 

Dr Habeeb ya ƙara da cewa zanga-zangar ba lallai ne ta haifar da ɗa mai ido ba idan ba a yi hankali ba, duba da abubuwan da suka faru a wassu ƙasashen Afirka.