Daga Yunusa Isa, Gombe
Ɗan takaran Jam’iyyar National Democratic Party (NDP) a zaɓen cike gurbi na mazaɓar tarayya ta Gombe-Kwami-Funakaye, Honourable Abdulmujib Abdulkarim Kwami, ya tabbatarwa al’ummar mazaɓar cewa zai yi musu wakilci na gari idan aka zaɓe shi a zaɓen da za a gudanar a ranar Asabar.
Da yake ganawa da manema labarai a Gombe, Honourable Abdulmujib ya bayyana cewa jagorancinsa zai fi mayar da hankali ne wajen kawo ci gaba ta hanyar yin ingantattun dokoki, inda zai sanya bunƙasa harkar noman zamani a gaba kasancewarsa babban sana’ar al’ummar mazabar.
“Kasancewar yawancin mutanenmu manoma ne, lokaci ya yi da ya kamata mu kawo musu da sabbin dabaru a harkar noma don inganta yawan amfanin gonan da suke samu da kuma tabbatar da samun wadataccen abinci a jiharmu,” inji shi.
Ɗan takaran ya kuma yi alkawarin gabatar da kudirorin doka da za su samar da ilimi kyauta don inganta shigar yara makarantu tare da ragewa iyaye ɗawainiya.
Bugu da kari, ya yi alkawarin mayar da hankali kan shirye-shiryen tallafawa mata da matasa ta hanyar samar musu ayyukan yi da tallafin jari don dogaro da kai ta fuskar sana’o’i da kasuwanci.
Da yake jawabi kai tsaye ga masu zabe, Honourable Abdulmujib ya yi ƙira ga al’ummar Gombe-Kwami-Funakaye su guji siyasar kuɗi, sannan ya gargaɗi matasa su guji shiga bangar siyasa ko su bari wassu bata garin ‘yan siyasa marasa kishi su yi amfani da su gabanin, lokacin ko bayan zaben cike gurbin dama babban zaben 2027 mai zuwa.
Ya kuma yi ƙira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar da gudanar da zabe mai inganci, a gaskiya da adalci, ta hanyar zama yar ba ruwanmu da kuma baiwa kowa damar fafatawa daidai wa daida, ya kara da cewa jam’iyyar NDP a shirye take tsaf don shiga zaben cike gurbi da ma zaben 2027.
Yace”Jam’iyyar NDP ta shirya fafatawa a zaben cike gurbin da kuma babban zabe na 2027″.

