Yunusa Isa, Gombe

 

Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Gombe Hon. Barista Rambi Ibrahim Ayala, ya yi maraba da umarnin babbar kotun tarayya dake Gombe, na hana uwar jam’iyyar na ƙasa sauya sunayen shugabannin jam’iyyar na gundumomi da ƙananan hukumomi da shugabannin jam’iyyar na jiha.

 

Da yake zantawa da manema labarai cike da farin ciki jin daɗi, Barista Rambi yace “Wannan umarnin kotun wata babbar nasara ce ga demokraɗiyyarmu”.

Da yake bayyana matakin uwar jam’iyyar a matsayin wanda ya sabawa doka da tsarin demokraɗiyya, shugaban NNPPn na jihar yace “Rusa shugabannin na jiha ba kawai ya saɓawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba ne, har ma da kundin tsarin mulkin ƙasarmu Najeriya na 1999”.

 

Yace ba tare da wata takardar sanarwa ko tuhuma kan wani laifi ba, suka wayi gari da wani saƙo da aka wallafa a shafukan sada zumunta cewa an rusa shugabannin jam’iyyar na gundumomi da ƙananan hukumomi da kuma na Jiha, lamarin da yace ya sanya suka garzaya kotu don neman a yi musu adalci.

Shugaban ya bayyana matakin uwar jam’iyyar da cewa zagon ƙasa ne na siyasa don kawo cikas ga jam’iyyar dake bunƙasa a jihar, wacce ke da cikakken tsarin shugabanci mai inganci a dukkan matakai.

 

Da yake ƙiran haɗin kai da kishin NNPP a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, Barrister Rambi ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa NNPP a jihar za ta ci gaba da samun nasara don kyautatuwar demokraɗiyya.

Yace ƙoƙari da jajircewarsu shi ne na ganin NNPP ta zama jam’iyya mai karsashi, ta yadda za ta yi gogayya kafaɗa da kafaɗa da jam’iyya mai mulki, har ma ta kwace mulki a zaɓen 2027.

 

Ƙoƙarin jin ta bakin Sulaiman Hamza, sakataren kwamitin riƙo wadda uwar jam’iyyar ta kafa don tafiyar da al’amuran jam’iyyar a jihar ya ci tura, saboda bai amsa ƙiraye-ƙirayen da aka yi masa a waya ba.

A ranar Litinin ce dai wata babbar kotun tarayya dake Gombe ta dakatar da uwar jam’iyyar ta NNPP ta ƙasa daga sauya sunayen shugabannin na NNPP na gundumomi da ƙananan hukumomi da shugabannin jam’iyyar na jiha a Gombe har sai an saurari karar da wasu mutane shida suka shigar a gaban kotun.

 

Umurnin ya biyo bayan buƙatu huɗu ne da masu gabatar da ƙarar suka shigar gaban kotun a ranar Juma’a.

 

A cikin umarnin, ta hannun mai shari’a T.G. Ringim, kotun ta amince da buƙatun farko dana biyu na masu ƙara, amma ta ki amincewa dana uku.

Kotun ta sanya ranar 27 ga watan Janairun 2025 don sauraron ƙarar.