Daga Yunusa Isa, Gombe
Jam’iyyar NNPP ta tabbatar da zaɓin da aka yiwa shugabanninta na gundumomi, ƙananan hukumomi dana jiha a matsayin cikakkun jagororin jam’iyyar a Jihar Gombe.
Da yake jawabi yayin amincewa da shugabannin riƙon, wakilin jamiyyar na ƙasa, Dr Oke Babatunde, yace sabbin shugabannin sun samu cikakken haɗin kai da goyon bayan jagorori da shugabannin jam’iyyar na ƙasa.
Dr Babatunde yace “Wannar tabbatarwa ta yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu, ina taya ku murnar kasancewa cikin wannar tafiya ta ceto Jihar Gombe daga tabarbarewar harkokin tattalin arziƙi da siyasa, nan ba da jimawa ba adalci zai tabbata. Wannan lokacinmu ne, kuma za mu ci nasara”.
Da yake bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta kafa gwamnati mai zuwa a Gombe, Dr Oke yace sabuwar tafiyar tana da zango uku da za ta nausa jihar; nasara, adalci da kuma ‘yanci.
A nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar ta NNPP a jihar Barista Rambi Ibrahim Ayala, yace tabbatar da su a matsayin cikakkun shugabannin ya biyo bayan giɓin shugabanci ne da aka samu a jam’iyyar tun daga gundumomi har zuwa jiha, lamarin da yace ya taimaka wajen koma bayan jam’iyyar a zaɓukan da suka gabata.
Rambi yace jim kaɗan bayan sauya sheƙar tsohon shugaban jam’iyyar na jiha, suka gano cewa jam’iyyar tana gudanar da harkokinta ne a ƙarƙashin ‘shugabannin jeka na yi ka’ waɗanda ya bayyana a matsayin jagororin bogi.
“Don ɗinke wannan babban giɓi, sashi na 30 na kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya yi tanadin cike gurbi, don haka abin da muke yi a safiyar yau ya dace da tanadin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP”.
Da yake jaddada goyon baya da biyayyarsu ga shugabannin jam’iyyar na ƙasa, Rambi ya bada tabbacin tafiya da kowa, yana mai cewa “Yanzu NNPP ta samu cikakken tsarin shugabanci kuma a shirye take ta lashe duk wani zaɓe da za a yi a Gombe”.
A sakonsu na fatan alheri, wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da mataimakin ɗan takaran gwamna na jam’iyyar a zaɓen 2023 Hon Hamma Abubakar Tanimu, da babban daraktan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a 2023 Dr Samaila Muhammad (Sa’in Dukku), da kuma Barista Audu Baba Kwami, sun buƙaci sabbin shuwagabannin cewa su zama jakadun jam’iyyar na ƙwarai, kuma su yi aiki cikin gaskiya da riƙon amana.
Yayin da suke bayyana giɓin shugabanci da rashin jagorori na gari a matsayin manyan dalilan da suka janyowa NNPP koma baya a 2023, dottawan jam’iyyar sun bayyana gamsuwa da sabin shugabannin, tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta taka rawar gani ta kuma yi nasara a duk wani zaɓe mai zuwa.
Kafin tabbatarwar dai sai da aka ƙira sunayen shugabannin riƙon na jaha, ƙananan hukumomi da gundumomi, tare da bada dama ga masu ƙorafi, neman ƙarin haske ko nuna rashin amincewa da su.
Wakilan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sun shaida yadda tabbatarwar ta gudana.