Daga Yunusa Isa, Gombe
Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) Reshen Jihar Gombe, ta kama wassu mutane bakwai da suka ƙware wajen yin takin zamani da ƙasa suna sayarwa manoman jihar da basu ji ba basu gani ba.
Da yake jawabi yayin da ya jagoranci tawagar manema labarai da jami’ai da dakarun hukumar zuwa wurin da ake haɗa takin a Anguwar Nasarawo Gombe, kwamandan hukumar a Gombe Muhammad Bello Mu’azu, yace waɗanda ake zargin sun fi yin wannan aika-aika nasu ne da dare.
Kwamanda Bello Mu’azu yace babban wadda ake zargin kuma mamallakin masana’antar haɗa takin ya ari na kare, yana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kuma nan ba da jimawa ba zai faɗa komar hukumar.
Ya shawarci manoman jihar su riƙa taka tsan-tsan wajen sayan taki don gujewa faɗawa tarkon yan algus.
“Ƙira na ga manomanmu shi ne su buɗe idanuwansu don sanin irin abin da suke saya, su bincika sosai, su jika takin da ruwa su muttsuka don tabbatar da cewa ba laka bace kafin su saya”.
“Idan za ku sayi taki, ku je wurin sanannun dillalai, don kaucewa asarar kuɗin ku wajen sayen laka,” in ji Bello Mu’azu.
Kwamanda ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin suna haɗa buhun taki urea na gaske ne guda ɗaya da ƙasa buhu biyar zuwa shida don haɗa takin na bogi.
Yayin da yake jaddada aniya da jajircewar hukumar wajen magance aikata laifuka da zamba a jihar, kwamandan yace da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotu don su girbi abinda suka shuka.
Da yake zantawa da manema labarai, manajan kamfanin haɗa takin na bogi Usman Abubakar, yace suna shigo da jar ƙasar ce da ake amfani da ita wajen yin takin na bogi daga Ƙanƙara ta Jihar Katsina.
“Muna amfani da taki na ainihi, mu gauraya shi da siminti, da ƙasa kala-kala da sauran abubuwa don haɗa takin na jabu,” inji shi.
Usman yace sun shafe fiye da shekara biyu suna wannar baƙar sana’ar a Kano, inda a kwanan nan suka buɗe sabon reshe a Gombe.
Yace kawo yanzu sun sarrafa tare da sayar da buhu fiye da 1,000 na ƙirƙirarren takin NPK 20-10-10 da sauransu a faɗin jihar, ɗauke da sunan ‘Dala Fertilizer’ akan kuɗi naira 22,500 a kowane buhu.