Daga Yunusa Isa, Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta rattaba hannu kan kwangilolin gina cibiyoyin sassan gwamnati uku da suka ƙunshi majalisar dokokin jiha da babbar kotun jiha na zamani, da gidan gwamna da ofishin jami’an tsaron Operation Hattara da kuma hedkwatar jami’an hukumar kula da harkokin tsaro, zirga-zirgar ababen hawa da alkinta muhalli ta Jihar Gombe (GOSTEC).

Da yake jawabi jim kaɗan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na jihar Dr Usman Maijama’a Kallamu, yace tun tuni ya kamata ace an yi waɗannan ayyuka duba da yanayin da babbar kotun jiha da majalisar dokokin jihar suke ciki.

Yace idan aka kammala ayyukan, za su ƙayata fadar jihar ta dace da sauran manyan biranen jihohin ƙasar nan.

Da yake ƙira ga kamfanonin da aka baiwa kwangilar su tabbatar da bin ka’idojin da aka zayyana tare da yin aiki mai inganci, kwamishinan yace gwamnatin jihar ba za ta lamunci durmuƙel a ayyukan ba.

Da yake taya kamfanonin murnar nasarar samun kwangilolin, Maijama’a ya buƙacesu su tabbatar sun kammala ayyukan a kan kari.

Ya kuma yi ƙira ga al’ummar jihar su ci gaba da yin addu’o’i da mara baya ga gwamnatin Inuwa Yahaya a ƙoƙarinta na ganin ta kawowa Jihar Gombe ci gaba.

Tun da farko a jawabinsa a madadin kamfanonin da aka baiwa kwangilar, Manajan Daraktan kamfanin A.D Sheriff & Investment Nigeria Limited Alhaji Abubakar Sheriff, ya yabawa gwamnatin jihar bisa ganin cancantarsu ta yin waɗannan kwangilolin, yana mai bada tabbacin cewa za su yi aiki mai inganci bisa ƙa’idojin da aka sharɗanta.

Da yake tsokaci a madadin kwararrun masu sanya ido kan ayyukan, Injiniya Taofik Popoola, ya bada tabbacin yin iyakacin bakin ƙoƙarinsu don tabbatar da aiki mai inganci da kuma kammala ayyukan a kan lokaci.

A nasa ɓangaren, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan ayyuka na musamman Architect Yakubu Mamman, yace za su sanya ido sosai kan ayyukan don tabbatar da cewa ba a yi almundahana a cikin su ba.

A jawabinsa na maraba, Daraktan Gine-gine a ma’aikatar ayyukan Builder Silvanus Silas, yace bada ayyukan yana nuni da himmatuwar gwamnatin jihar na ƙarfafa demokraɗiyya, yana mai cewa idan aka kammalasu, ayyukan za su saita ci gaban jihar a nan gaba.