
…Yace APC ta Ƙara Karfi da Haɗin Kai, Don Amfanin Al’ummar Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karɓi Sanata mai wakiltar Kudancin Gombe a Majalisar Dokoki ta Kasa, Sanata Anthony Siyako Yaro zuwa cikin Jam’iyyar APC bayan ya fice daga Jam’iyyar PDP.
Wata sanarwa da mai taimakawa ɗan majalisan kan harkokin sadarwa da dabaru, Yahaya Joel Musa ya sanyawa hannu kuma ya miƙa ta ga jaridar Jewel Times, ta ce Sanata Yaro shi ne sabon jigon da ya shiga APC ƙarƙashin jagorancin Gwamna Inuwa Yahaya.
Da yake jawabi a wurin karɓar sanatan, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shigar Sanata Anthony Yaro APC a matsayin “babban ci gaba a fagen haɗin kai da ci gaban Gombe ta Kudu.”
Yace “A yanzu APC ta ƙara ƙarfi da haɗin kai, tare da ƙarfin cimma burin duk al’ummar Gombe. Muna maraba da Sanata Anthony Siyako Yaro ba a matsayin baƙo ba, amma a matsayin abokin tafiya wajen gina Jihar Gombe mai albarka”.
A jawabinsa, Sanata Siyako Yaro ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa kyakkyawan jagoranci da kyakkyawar tarbar da ya yi masa.
Yace shawararsa ta shiga APC ta samo asali ne daga buƙatar daidaita Gombe ta Kudu da gwamnatin Tarayya don samar da kyakkyawan wakilci da ci gaba mai ma’ana.
Sanata Yaro ya jaddada cewa “Ban zo APC don kwace wani abu daga wurin wani ba. Na zo ne don bada gudunmawa da yin aiki tare da shugabannin jam’iyya don ci gaban al’ummarmu. Gombe ta Kudu ce ta farko a kullum”
Hakan dai ya biyo bayan nasarar da gwamnan ya samu ne na janyo ƴan majalisan tarayya uku cikin APC daga jam’iyyun adawa, waɗanda suka haɗa da; Mataimakin Shugaban Marassa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Hon. Ali Isa JC; da Hon. Abdullahi El-Rasheed mai wakiltar Mazabar Tarayya ta Dukku/Nafada; da kuma Hon. Inuwa Garba mai wakiltar Mazabar Tarayya ta Yamaltu-Deba.
Sanarwar tace “Waɗannan ficewar ‘yan majalisa sun ƙara ƙarfafa ikon APC a Jihar Gombe gabanin babban zaɓen 2027”.
Wadanda suka halarci taron tarbar sanatan sun haɗa da Babban Mai tsawatarwa na Majalisar Wakilai ta 10, Rt. Hon. Usman Bello Kumo, da Mataimakin Sakataren Kuɗi na Ƙasa na Jam’iyyar APC, Hon. Hamma Adama (Dattuwa) Ali Kumo.
