Daga Yunusa Isa, Gombe

 

Shugaban Matasa na Ƙungiyar Dottawa da Matasan Arewa (AYEF) Hon. Nafi’u Usman Bello (Scorpion) ya fara tattaki daga Gombe zuwa Abuja, don yin ƙira ga tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami akan ya fito takaran gwamnan Jihar Gombe a 2027.

 

Da yake jawabi ga manema labarai kafin fara tattakin daga babban shataletalen Gombe, Scorpion yace maƙasudin tattakin shine yin ƙira ga Pantami yazo ya ceci Gombe a 2027.

Nafi’u Scorpion wanda kuma shine Babban Sakataren Ƙungiyar Ƴan Gwagwarmaya a Kafafen Yaɗa Labarai na Jahar Gombe, yace “Farfesa Pantami ya fi kowa cancantar tsayawa takara a zaɓen 2027 a Jihar ta Gombe. Wannan ya ƙara min ƙwarin gwiwar fara wannan tattaki, don gamsar da shi ya fito takarar gwamna a jiharmu ta Gombe duba da irin tarihin da ya kafa a lokacin da yake Babban Daraktan Hukumar NITDA, da kuma lokacin da ya yi minista, nasarorin da ya samu ba su da adadi”.

 

Scorpion yace tattakin na al’ummah ne ba na ƙashin kansa ba.

Ya ƙara da cewa “A matsayina na wakilin jama’a, zan kai saƙonsu ne zuwa Abuja ga tsohon ministan akan ya zo ya ɗora daga nasarorin wannar gwamnatin”.

 

Da yake ƙira ga ƴan siyasa da sarakuna da shugabannin al’umma da malaman addini a jihar cewa su matsawa Pantami lamba har sai ya fito neman takara, Nafi’u Usman yace zai ci gaba da zama a Abuja daga yanzu zuwa shekara guda, har sai tsohon ministan ya amince zai tsaya takara.

 

“Zan ci gaba da zama a Abuja har sai haƙata ta cimma ruwa, idan kuma Farfesa Pantami ya ƙi amincewa, to mun shirya duk wassu takardun da ake bukata don gurfanar da shi a gaban kotu, don tilasta masa miƙa wuya wa hidimar al’umma.

Shugaban matasan ƙungiyar ta AYEF na ƙasa yace zai yi tattakin ne a hankali kuma ido na ganin ido daga Gombe zuwa Bauchi, ya bi ta jihohin Filato da Nasarawa, inda yake fatan isa babban birnin tarayyar a ranar Talata ko Laraba.

 

Manazarta sun yi imanin cewa Pantami da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC suna zawarcin kujerar ta gwamna don maye gurbin Gwamna mai ci Muhammadu Inuwa Yahaya a zaɓen 2027.