Daga Yunusa Isa, Gombe

Al’ummomin garin Lasani da Potede dake gundumar Tal a Ƙaramar Hukumar Ɓillliri, sun bayyana matuƙar godiya da jin daɗinsu ga ƙungiyar Hope Springs International, dake ayyukanta a Nijerya ta hannun ƙungiyar Servants of Hope Initiative bisa kawo musu ƙarshen matsalar ruwan sha da suka kwashe shekaru da dama suna fama da shi.

A yayin bikin miƙa rijiyoyin burtsatsen biyu da ƙungiyar ta samar, al’ummomin ƙauyukan sun nuna jin daɗinsu, suna masu cewa tun kafuwar ƙauyukan nasu tsawon shekaru, sun dogara ne ga kwarurruka don samun ruwa.

Wani dattijo a ƙauyen na Lasani Nitte Dansalla, yace “A yanzu sauƙi ya zo mana, domin ba mu taɓa tsammanin hakan ba a halin yanzu. Saɓanin ‘yan siyasan da suka sha yi mana alkawarin ruwa da sauran su ba tare da sun cika ba, Hope Springs International bata yi mana alkawarin komai ba, sai kawai muka ga famfo. A yau ga ruwa yana gudana karon farko a Lasani, muna godiya matuƙa”.

Da suke jawabi a madadin matasan Lasani, Mela Solomon, da Liyatu Ilu wacce ta yi jawabi a madadin mata, sun yabawa ƙungiyar bisa ceto su daga cututtukan dake lakume rayuka duk shekara.

Hakazalika, wani dattijo a ƙauyen Potede kuma shugaban ƙungiyar ci gaban ƙauyen na Potede Maliki Adamu, yace famfon shine aiki na farko da wata ƙungiya ko gwamnati ta taɓa aiwatarwa a ƙauyen.

Haka ma James Tula da Rose Obeth waɗanda suka yi jawabi a madadin matasa da matan ƙauyen, sun yi addu’ar Allah ya sakawa Hope Springs International da jami’anta.

“Muna addu’ar Allah ya saka muku da mafificin alheri kasancewar mun fidda rai daga samun ruwan sha, amma Hope Springs International ta farfaɗo tare da aiwatar da mafarkin da muka daɗe muna yi na samun ruwa”.

A jawabinsa yayin miƙa ayyukan, shugaban ƙungiyar ta Hope Springs International Lee Hodges, wanda Daraktan ayyuka na ƙungiyar a Afirka Barista Rambi Ibrahim Ayala ya wakilta, yace ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, manufarta kawai ita ce ta tsamo al’ummomin da aka barsu a baya daga wahalhalu da suke fama da su ta hanyar ayyukan jin ƙai.

Yace “Hope Springs International ta fi mai da hankali ne kan yankunan da aka barsu a baya a fannoni abubuwan more rayuwa kamar ruwan sha da asibitoci da makarantu”.

Daraktan ya buƙaci al’ummomin kauyukan su sanya ido tare da kula da ayyukan yadda ya kamata.

“Kada ku bari waɗannan famfuna su tsaya saboda yan matsalolin da basu taka kara sun karya ba, ku kafa kwamiti mai ƙarfi da zai riƙa sanya ido kan famfunan, an yi su ne don ku, ku yi amfani da su yadda ya kamata,” in ji shi.

Da yake ƙarin haske kan hakan, wani ɗan asalin yankin na Tal Injiniya Mela Lashiru, yace “Ba za mu ƙara biyewa ‘yan siyasan romon baka ba, waɗanda basa tunawa da mu sai lokacin yakin neman zaɓe. Ba mu roƙi waɗannan ayyuka ba, amma waɗannan mutane suka ga mun cancanci su kawo mana ɗauki don fitar da mu daga waɗannan wahalhalu don muma a tafi da mu kamar kowa”.

Alummomin ƙauyukan sun cika da murna da farin ciki, yayin da suka yi ta raye-raye da rera wakokin yabo ga ƙungiyar ta Hope Springs International da jami’anta.