…Ya Buƙaci a bi Tsarin Mulki
Daga Yunusa Isa, Gombe
Ɗan takaran gwamna na Jam’iyyar Labour (LP) a Jihar Gombe, AIG Muazu Halilu Zubairu (Mai Ritaya), ya yi watsi da iƙirarin da Alhaji Muhammad Jibrin Danbarde yake yi na shugabancin jam’iyyar a jihar, yana mai cewa dole ne a warware taƙaddamar shugabancin jam’iyyar ta hanyar tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta.
Da yake jawabi ga manema labarai a Gombe, Zubairu ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon sauya sheƙar da zababben shugaban jam’iyyar na jihar Mista Ezra Jatau ya yi zuwa Jam’iyyar PDP, wanda hakan ya haifar da gurbi a shugabancin jam’iyyar.
Yace cike gurbin da babu kowa da kuma tantance shugabanni na jihar dole ne su dace da Sashi na 15 da na 16 na kundin tsarin mulkin Jam’iyyar ta Labour.
AIG Zubairu ya zargi Ɗanbarde da ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar tare da gabatar da ‘yan ƙungiyar siyasarsa ta Ɗanbarde Movement a matsayin shugabannin bayan ficewar Jatau.
“Ina bayyanawa ƙarara cewa ƙungiyar Muhammad Jibrin Ɗanbarde ba jam’iyyar Labour ba ce, kuma Jam’iyyar Labour ba ƙungiyarsa ba ce,” in ji Zubairu.
“Duk da cewa ƙungiyarsa tafiya ce ta siyasa don haɓaka muradun siyasa na mutum ɗaya, Labour Party jam’iyyar siyasa ce mai tsari da sassa kamar yadda aka tsara a cikin tanadin kundin tsarin mulkinta.”
Ɗan takaran gwamnan ya jaddada cewa ko da ‘yan ƙungiyar Ɗanbarde suna cikin jam’iyyar Labour, mafi yawan magoya bayan jam’iyyar a jihar Gombe basa cikin ƙungiyar kuma suna da haƙƙi a harkokin jam’iyyar.
A cewarsa, majalisar gudanarwar jam’iyyar ta jiha tana hidima ne wa dukkan membobinta kuma ta samu sahihancinta ne kawai daga tsarin da kundin tsarin mulki ya kafa.
Saboda haka ya yi gargaɗi ga Danbarde da ya daina gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha ko ɗora yaransa a shugabancin jam’iyyar, yana ƙalubalantarsa da ya gabatar da duk wata shaida ta ikirarinsa ga hukumomin jam’iyyar da suka dace.
Zubairu ya kuma yi ƙira ga shugabannin jam’iyyar ta Labour na kasa su shiga cikin lamarin da gaggawa, su warware matsalar bisa bin tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, sannan su sanar da jama’a shawarar da suka yanke a hukumance.
“Ina ƙira ga membobi da magoya bayanmu su kwantar da hankalinsu, su guji kai hare-hare ko tsangwama, sannan su tantance duk ata sanarwar da ake takaddama a kanta daga majiyoyin jam’iyyar,” in ji shi, yana mai cewa ɗaukar matakin gaggawa zai baiwa jam’iyyar damar mai da hankali kan yi wa al’ummar jihar Gombe hidima.
