Skip to content
Jewel Times
Menu
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Privacy Policy
  • Sample Page
  • Terms and Conditions
Menu

Jigo a APC ya Kawo Karshen Rashin Wuta na Watanni 8 a Kauyukan Amada 8, ya Nemawa Tinubu da Yan Takaran APC Goyon Baya

Posted on November 21, 2026November 21, 2026 by Jtimes

Daga Yunusa Isa, Gombe

Murna ta mamaye fuskokin jama’ar wassu ƙauyuka tara a Ƙaramar Hukumar Akko ta Arewa a Jihar Gombe, yayinda wani jigon APC, Shamsuddeen Daudu Umar Abdussalam, ya biya kuɗin gyaran randar wutar lantarki (transformer) na yankin data lalace, inda ya kawo ƙarshen zamansu cikin duhu na tsawon watanni takwas ƙauyukan.

Da yake jawabi yayin wani taro a Garin Gamadadi, Abdussalam, wanda shi ne mu’assasin ƙungiyar Three Star Group mai goyon bayan APC – ya bayyana cewa ya samar da tallafin ne na Naira miliyan 1 da dubu 500 don dafawa shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Sabunta Fata da kuma ƙoƙarin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na faɗaɗa samar da tsayayyiyar wutar lantarki.

A cewar Abdussalam, wannar gudunmowa tana kuma da nufin neman goyon bayan jama’a ga Jam’iyyar APC da kuma goyon bayan Shugaba Tinubu, da ɗan takaran gwamna na jam’iyyar Dr. Jamil Isyaku Gwamna, da sauran ‘yan takaran APC gabanin babban zaɓen 2027.

Ya buga misali da ayyukan more rayuwa da dama da gwamnatocin tarayya data jiha ke gudanarwa, yana mai ƙira ga al’ummar yankin, musamman mata da matasa su goyi bayan jam’iyyar don ci gaba da samun romon dimokuradiyya.

“Wannan wani ɓangare ne na gudummawarmu don dafawa Sardaunan Gombe da duk ‘yan takaran APC a 2027,” in ji Abdussalam, yana mai tabbatar da cewa ya kammala biyan kuɗin gyaran randar wutar na Naira miliyan 1 da dubu 500 don tabbatar da dawowar wutar lantarki nan take.

Da yake jawabi a madadin waɗanda suka amfana, Shugaban Kwamitin Gyaran Transfoman, Alhaji Tela Yau, ya bayyana katsewar wutar na tsawon watanni takwas a matsayin mawuyacin lokaci wadda ya gurgunta rayuwar jama’a da harkokin tattalin arziki a yankin.

Yace duk ƙoƙarin da suka yi na neman a gyara randar wutar ya ci tura har sai da Abdussalam ya kai musu ɗauki.

“Mun yi fafutuka da faɗi tashi muna neman taimako don gyara wannan tarasfoma ba tare da samun nasara ba, har sai da Shamsu Daudu Umar ya zo ya dafa mana,” in ji Yau, yana mai ƙarawa da cewa tarihinsa da suka samu na bada gudummawa ga ci gaban al’umma yasa wannan gudunmawar ba zo musu da mamaki ba.

A sakonninsu na fatan alheri, jigo a Jam’iyyar APC a yankin Abubakar Bello Gamadaɗi da shugabannin al’umma da suka haɗa da Muhammad Jauro Akko (Yamanga), da Alhaji Rabi’u, Alhaji Musa Abdullahi, da Hon. Aliyu Ibrahim Akko, sun yabawa Abdussalam bisa jajircewarsa ga ci gaban yankin.

Da suke alƙawarin goyon bayansu ga jam’iyyar, shugabannin sun yi ƙira ga al’ummar yankin su yi watsi da yaudarar da ‘yan adawa ke yaɗawa, su zaɓi jam’iyya mai mulki a dukkan matakai.

“Za mu zaɓi APC daga sama har ƙasa – Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, Jamil Gwamna a matsayin gwamna, Muhammad Ahmadu (Jarman Deba) a matsayin sanata, Usman Bello Kumo a matsayin ɗan majalisar wakilai, da Musa Wuro Biriji a matsayin ɗan majalisar jiha,” in ji shugabannin, suna masu jaddada cewa “zaɓar APC zaɓen ci gaba mai ɗorewa ne garemu a wannan yankin.”

Shi ma da yake jawabi a wurin taron, Hakimin Amada, Alhaji Ɗanahiru Abdulkadir Abdulsalam, ya yaba da karamcin wadda ya bada gudummawar, yana mai cewa ya gaji halin taimako ne daga mahaifinsa. Ya yi ƙira ga sauran ‘yan asalin yankin su yi koyi da Abdussalam ta hanyar zuba jari a fannin jin daɗin al’umma.

Don nuna jin daɗinsa ga gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban yankin, daiacin Garin Gamadaɗi, Alhaji Sanusi Abdulkadir, ya baiwa Shamsu Daudu Umar Abdussalam hagalaren “Chiroman Gamadaɗi”.

Wannan tallafi na maido da wutar lantarki ya kawo sauki ga ƙauyukan yankin guda tara, wato: Garin Gamadaɗi, Garin Marori, Malam Jamo, Jauro Baba, Garin Konkejo, Garin Jauro Manuwa, Jauro Hammadu, da kuma Jauro Libidi.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Jigo a APC ya Kawo Karshen Rashin Wuta na Watanni 8 a Kauyukan Amada 8, ya Nemawa Tinubu da Yan Takaran APC Goyon Baya
  • ADC Moves to Consolidate Unity in Bayo as Usman Garba Promises Education, Welfare Reforms.
  • Gombe NSCDC Commandant Tours Divisions, Warns Officers Against Extortion, Indiscipline
  • 2027: Gombe APC Inaugurates 35-Man Legal Directorate
  • Harvest of Heritage: Gombe Igbo Community in Joy for Annual New Yam Festival

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Children
  • Culture
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Human Capital Development
  • Infrastructure
  • Justice
  • Law
  • Livestock
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme