Daga Yunusa Isa, Gombe

Hukumar Tsaro Ta Civil Defence (NSCDC) Reshen Jihar Gombe ta yi holen wassu mutane 14 da take zargi da laifin ƙwacen waya da kuma lalata.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin, Kwamandan Hukumar a Jihar Muhammad Bello Muazu ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar SC Buhari Sa’ad, yace an kama waɗanda ake zargin ne a gidajen saukar baƙi da otal-otal da tsakar dare a Gombe.

Yace biyo bayan haramcin da gwamnatin jihar ta sanya kan harkokin gidajen gala da kulob-kulob din dare, waɗanda ake zargin sun sauya akala zuwa wasu wurare, inda suke aikata munanan harkokinsu a gidajen baƙi.

Jami’in hulɗa da jama’an yace “Mun kama biyu daga cikin waɗanda muke zargin ne da laifin ƙwacen waya, wassu huɗu kuma a gidan Sifeta Hassan dake BCGA da misalin karfe 1:08 na dare, yayin da sauran takwas ɗin maza da mata kuma aka kama su ne a Travelers Lodge Gombe da misalin karfe 1:57 na dare, inda aka samu waɗanda ake zargin suna baɗala.

Da yake jaddada aniyar rundunar na daƙile ayyukan alfasha, da sauran laifuka a jihar, Buhari ya bukaci goyon bayan al’ummar jihar don kakkaɓe bata gari a jihar.

Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu don su fuskantar hukunci.

Wasu daga cikin waɗanda ake zargin, sun danganta abinda suka aikata da son zuciya da ruɗin shaiɗan, suna masu alƙawarin kauracewa irin wannan alfasha, tare da zama na gari a cikin al’umma.