…Yayinda Jihar Ta Yaba Da Sabin Dabarun Tara Kuɗaɗe
Gamayyar Kungiyoyin Alurar Rigakafin Cututtuka (VNDC) ta buƙaci Gwamnatin Jihar Gombe da ta ɗauki nauyin gudanar da rigakafi ga yara don rage yawan yaran da ba a taɓa yiwa rigakafi ba a jihar.
Shugabar ayyuka da shirye-shirye ta gidauniyar Misis Chika Nwankwo ce ta yi wannan roko jiya Laraba yayin da tawagarta ta gana da babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe Pharmacist Mohammed Jalo.
Wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta ma’aikatar lafiya ta jihar Hauwa Salami ta sanyawa hannu kuma ta mikawa gidan rediyon Amana, tace Misis Nwankwo ta yi ƙarin haske kan ƙalubalen kuɗaɗen da ƙasar nan ke fuskanta, lamarinda yasa ta gaza fitar da kuɗaɗen rigakafin da aka keɓe yadda ya kamata, da kuma ƙaruwar yaran da ba a taɓa yiwa rigakafi ba a ƙasar nan.
Tace “Tun da Jihar Gombe na ɗaya daga cikin jihohi 18 dake da yaran da ba a taɓa yiwa rigakafi ba, yana da muhimmanci gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin a shirye-shiryen rigakafi gabanin janyewar ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji kan harkokin rigakafi”.
Da take bayyana irin ayyukan da gamayyar ta gudanar da cewa sun haɗa da ganawa da hukumar lafiya matakin farko ta ƙasa da ma’aikatun lafiya, kuɗi data kasafi da tsare-tsare, Mrs Nwankwo ta bada shawarar ɗaukan dabarun samar da kuɗaɗe a cikin gida, kamar yadda wassu jihohi irinsu Legas, Ogun da Delta suka yi.
A nasa jawabin, Babban Sakataren ma’aikatar lafiya ta Jihar Pharmacist Muhammad Jalo, ya yabawa tawagar, yana mai bayyana jin daɗinsa kan dabarun samar da kuɗaɗe a cikin gida da tawagar ta bada shawara.
Yace “Wannar ta aiwatar da abubuwa da dama a fannin lafiya da suka haɗa da farfaɗo da cibiyoyin lafiya matakin farko 114 (ɗaya a kowace gunduma ta jihar)”.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Inuwa Yahaya ta kuma gyara asibitin kwararru na jiha, kuma yanzu haka tana aiki a kan wassu manyan asibitoci uku, ɗaya a kowacce mazaɓar sanata.
Babban Sakataren ya bada tabbacin yin aiki tare da gamayyar ƙungiyoyin don cimma burin da aka sanya a gaba na rage yawan yaran da ba a taɓa yiwa rigakafi ba a jihar.
Taron wanda ya gudana a ma’aikatar lafiya ta jihar, wani ɓangare ne na ayyukan tuntuɓa da bada shawarwari da gamayyar ta VNDC ta shirya don yin haɗin gwiwa a shirin samar da rigakafi ga yaran da ba a taɓa yiwa ba (PREACH Project).
Shirin wadda ke samun tallafi daga rukunin ƙasashe masu samar da rigakafi da ake ƙira GAVI, yana bada tallafi ne ta ƙarƙashin shirin Tuntuɓa da Bada Shawarwarin Kiwon Lafiya na Duniya (GHAI), wadda ya ƙuduri aniyar faɗaɗawa da ƙarfafa gwiwar masu ruwa da tsaki kan harkokin rigakafi da ƙarfafa harkokin kiwon lafiya matakin farko ta hanyar ririta yan kuɗaɗen da ake tarawa a cikin gida.
Ya kuma ƙuduri aniyar ƙarfafa samar da kuɗaɗe daga cikin gida don yin rigakafi, da tabbatar da gaskiya da adalci wajen alkinta kuɗaɗe, da sakin kuɗaɗen rigakafin a kan lokaci, gami da ɗabbaƙa ka’idoji da sharuɗan gamayyar ta a Gavi.