Daga Yunusa Isa, Gombe

Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ta bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a fara karatu a reshenta dake Dukku a matsayin Tsangayar Kimiyyar Muhalli.

Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar Sanata Joshua Lidani ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai kan nasarorin da jami’ar ta cimma.

Lidani yace, “Biyo bayan amincewar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi na kafa tsangayar jami’ar a makarantar da aka tsara tun farko a matsayin kwalejin jinya a Dukku, yanzu haka an kammala aikin inda reshen zai fara aiki a matsayin Tsangayar Kimiyyar Muhalli na Jami’ar Jihar Gombe. Za a ɗauki sabin ɗalibai a tsangayar nan gaba kaɗan.”

Da yake yabawa gwamnatin jihar bisa farfaɗo da fannin ilimi, shugaban yace makarantun sakandaren jihar da aka inganta, da sabin manyan makarantu biyar da aka ƙirƙiro zasu riƙa samarwa GSU da sauran jami’o’i ɗalibai masu nagarta.

Da yake tsokaci kan nasarorin da jami’ar ta cimma, Sanata Joshua Lidani yace majalisar gudanarwar jami’ar ta amince da ƙarin girma wa malamai 107, inda 4 daga cikinsu suka zama farfesoshi, 18 kuma zuwa matsayin ‘reader’, yayin da wasu 85 suka samu ƙarin girma zuwa matakai daban-daban.

Yace majalisar ta kuma amince da ƙarin girma wa ma’aikatan da ba malamai ba su 57 zuwa mutakai daban-daban.

Shugaban ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa haɗin kai da goyon bayan da yake baiwa jami’ar, lamarin da yace ya sa jami’ar ta GSU ta yi fintinkau ga sa’ointa a Najeriya.