Daga Yunusa Isa, Gombe

A ƙoƙarinta na magance matsalar tsaro a cikin al’umma, rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar cibiyar Thrive Trek Entrepreneurs Centre da tallafin gwamnatin jihar, sun ƙaddamar da wani shirin horas da sana’o’i na sati biyu ga wasu tubabbun matasa ‘yan kalare 20 da suka jima suna ta’asa a jihar.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin bada horon a hedkwatar ‘yan sandan jihar, kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Hayatu Usman, yace, “Kame, da gurfanar da matasan nan a gaban kotu dama tsaresu a gidajen yari kaɗai ba zai iya magance mana matsalolin tsaron da muke ciki ba, dole ne mu ɗauki wasu matakan, (na a ciza a fura) da kuma jawo matasan a jiki, waɗanda su ne mafiya yawan masu aikata waɗannan laifuka, don mu tallafa musu a fannonin ilimi, da wa’azi da koyar da su sana’o’in dogaro da kai”.

CP Hayatu ya ci gaba da cewa tuni matakin ya fara haifar da ɗa mai ido a fadar jihar, domin fiye da matasa ƴan kalare 250 ne suka watsar da makamansu suka rungumi zaman lafiya.

Ya yabawa cibiyar ta Thrive Trek bisa goyon bayan wannan yunƙuri, yana mai bada tabbacin cikakken goyon bayan rundunar don cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Da yake ƙira ga sauran ƙungiyoyi su dafawa wannan yunƙuri, kwamishinan ya ƙarfafi gwiwar masu hannu da shuni a cikin al’umma da cewa su tashi tsaye wajen ganin Jihar Gombe ta samu zaman lafiya da ci gaba ta hanyar marawa irin waɗannan yunƙuri baya.

A nasa ɓangaren, mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro AIG Zubairu Mu’azu (mai murabus), yace gwamnatin jihar tana yin dukkanin mai yiwuwa wajen ganin ta tallafawa matasa ta hanyar shigar da su cikin sana’o’i da ayyuka daban-daban kamar aikin samar da tsaro da kula da zirga-zirgar ababen hawa da alkinta muhalli na GOSTEC, da kuma kafa makarantar horar da matasa dake Boltongo.

Yace makarantar wacce ta kai kaso 90 cikin ɗari na kammaluwa, za ta iya horar da matasa fiye da 200 kan sana’o’i daban-daban a lokaci guda, yana mai cewa idan ta kammala, makarantar za ta zama babbar cibiyar horar da tubabbun yan kalaren jihar.

AIG Mu’azu ya kuma tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na ganin shirin ya yi nasara.

 

A nasa ɓangaren, wani fitaccen malamin Addinin Musulunci a Gombe, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro wanda ya ɗauki lokaci yana nasiha ga matasan, ya ja kunnensu su jajirce kan wannan horo, su kasance masu riƙon amana, kuma su guji cutan kowa.

Ya kwaɗaitar dasu, su kasance masu bin addini sau da ƙafa, da neman ilimi da kuma yin sana’o’in dogaro da kai, yana mai cewa hakan zai sa su zama ‘yan ƙasa nagari, su kuma cimma duk wani burinsu na rayuwa.

Da yake yabawa ƙoƙarin rundunar ‘yan sandan da kuma cibiyar, Sheikh Dokoro ya yi ƙira ga gwamnatin jihar ta ba da fifiko ga irin waɗannan tsare-tsare ta hanyar fitar da isassun kuɗaɗen da za a faɗaɗa shirin don ya kai ga ɗimbin matasa a jihar.

Tun farko da yake jawabi, shugaban cibiyar ta ‘Thrive Trek Entrepreneurs Centre’ Aliyu Babangida (National), yace cibiyar wacce ta ƙunshi kamfanoni bakwai, ta gamsu da yadda matasan suka himmatu kan tafarkin zaman lafiya, don haka ta yanke shawarar horar da su sana’o’in dogaro da kai don ɗorewar zaman lafiya da tabbatar da cewa basu koma ga tsohuwar sana’arsu ta kalare ba.

Aliyu yace fannonin da zasu horar da matasan sun haɗa da yadda ake aikin wayarin din lantarki da yadda ake dasa na’urorin samar da wuta daga hasken rana (solar) da dasa kyamarar tsawo ta CCTV da dai sauransu.

Matasan da suka fito daga unguwanni daban-daban na cikin garin Gombe, sun yabawa rundunar ‘yan sanda da cibiyar da kuma gwamnatin jihar bisa wannan yunkurin na sauya musu rayuwa, tare da bada tabbacin maida hankali kan sabin sana’o’in da za a koya musu.

Tsofin ‘yan kalaren sun bayyana cewa zaman banza da talauci ne manyan dalilan da suka jefa su ga aika-aikar ta kalare a jihar.