Daga Yunusa Isa, Gombe
Yayin da watan Ramadana ke ƙara ƙaratowa, an buƙaci mata Musulmi a Gombe su ruɓanya ƙoƙari wajen ayyukan alheri, da yafiya, ciyar da mabuƙata, da marassa galihu, kuma su kasance masu biyayya ga mazajensu, musamman a cikin watan mai alfarma.
Sheikh Murtala Saleh Kaugama ne ya yi buƙatar hakan yayin wata lakcar da Makarantar Kauthar Integrated Academy dake Sirankewo ta shirya a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen tarbar watan na Ramadan.
Sheikh Kaugama yace azumin Ramadan, kasancewarsa ɗaya daga cikin rukunan Musulunci, Allah ya wajabta shi akan Musulmi ne don su kasance masu taƙawa.
Da yake yi wa matan nasiha kan su shiga watan na Ramadana da tsarkakakken tunani ba tare da gaba ko riƙo da wani ba, malamin ya ƙarfafa musu gwiwan yafewa juna musamman a watan mai alfarma.
Sheikh Murtala ya yi musu albishir game da falalar ciyar da gajiyayyu da mabuƙata da marasa galihu a watan Ramadan, musamman idan aka yi la’akari da halin ƙuncin da ake ciki a yanzu.
Ya jaddada cewa ciyar da mabuƙata a watan Ramadan yana da falala da lada mai yawa, wanda ya ninninka na sauran watanni.
Ya kuma kwaɗaitar da su kar su raina ɗan abin da suke da shi, su tuna da wassu, domin abin sadakan da suke renawa yana iya kare su daga azabar wuta.
Malamin ya kuma shawarci mata su yawaita sallolin nafila, musamman qiyamul laili, da karatun Alqur’ani da yawaita salati ga Annabi SAW, da sauran ayyukan alheri.
Yace “Duk wanda ya dace kuma ya raya daren Lailatul Qadri da ibada, zai samu ladan fiye da ibadar watanni dubu”.
Da yake kwaɗaitar da matan su kasance masu hidima da biyayya ga mazajensu, malamin ya gargaɗesu kan su guji duk wani abu da zai iya lalata musu azumi.
A jawabinsa na godiya, shugaban makarantar ta Kauthar Integrated Academy Ustaz Usman Shuaibu ya bayyana godiya da jin daɗinsa ga Sheikh Murtala Kaugama bisa gabatar da lakcar, yana mai addu’ar Allah ya saka masa sa mafificin alheri.
Ya kuma yi ƙira ga matan da suka halarci wa’azin su yi amfani da abinda suka ji, inda ya bada tabbacin cewa makarantar za ta ci gaba da shirya irin waɗannan lakcoci don wayar da kan mata da fahimtar da su yadda zasu kyautata addininsu.