Skip to content
Jewel Times
Menu
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Sample Page
Menu

Na Dinke Barakar da a’ke samu yayin bikin Mauludi da Wakokin Yabon Fiyayyen Halilta.

Posted on March 7, 2024March 7, 2024 by Jtimes

La’akari da yadda masu wakokin yabon Fiyayyen Halilta wato (Sha’irai) a jihar Bauchi keyi an samar da tartibiyar mafita gare su wanda zai alkinta wannan fanni na yabo domin tabbatar da haɗin kai tsakanin Al’ummar Musulmai.

Sarkin Kasidun Bauchi,Alh. Muhammad Tukur Mato ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai dangane da shirye-shiryen bikin cikar shi shekaru biyu (2) da samun sarautar Sarkin Kasidun Bauchi.

Ya bayyana cewar cikin shekaru biyu da suka gabata ya shirya taron kara wa juna sani wa Sha’irai dake jihar Bauchi domin sanin ire-iren kalamai da Mawakan zasu keyi yayin yabon fiyayyen halirta.Alh. Muhammad Tukur ya gano cewar yaki da kalaman da basu dace wajen yabon Annabi (S.W.A) ko shakka babu suna kawo koma baya ga rayuwar al’umma, yana cewar dole suka tashi tsaye domin wayar da kai tare da sanya linzami ga Mawakan musamman Mawaka Mata a jihar.

Sarkin Kasidun Bauchi ya cigaba da cewar Gwamnatin Jihar Bauchi cikin shekarun da suka ga bata ta dauki nauyin gudanar da bikin Mauludin Fiyayyen Halilta tare da gudanar da addu’ah wa jihar Bauchi, a Gandun Dajin Yankari wanda hakan abun ya bawa ne.

Ya kuma yi amfani da wannan damar Inda ya bukaci sauran Sha’irai a jihar Bauchi da sauran Jihohin Tarayyar Najeriya dasu kasance masu bin koyaswar addinin Islama tare da neman Ilimi ga banin rera baituka wa Shugaban Halilta Annabi (S.A.W)Daga karshe ya mika godiyar shi ga Sarkin Bauchi Alh. Dr. Rilwanu Suleiman Adamu bisa mara mishi baya tare da nuna kauna ga sha’anin yabon Annabi (S.A.W) Yace Maimartaba Sarkin Bauchi ya chan chan ci yabo bisa tabbatar mishi da wannan sarauta mai albarka, shekaru biyu da suka shude.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bala Wunti Support Organisation Empowers Blind, Deaf with Entrepreneurial Skills
  • NEDC Bolsters Journalists’ Welfare with Ramadan Food Support
  • Ramadan: BWSO Donates Cash, Food Items to People with Disabilities in Bauchi
  • Gana Aliyu Emerges Gombe IPAC Chairman as New Executive Council Takes Office
  • FRSC Issues Red Alert as Haze Envelopes Gombe Roads

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme