Skip to content
Jewel Times
Menu
  • Gombe Social Investment Coordinator Visits Progress Radio, Seeks Collaboration
  • Sample Page
Menu

Masana Sun Bukaci Malaman Addini a Gombe Su Rungumi Dabarun Zamani Don Magance Labarun Bogi

Posted on April 11, 2026 by Jtimes

 

Daga Yunusa Isa, Gombe

 

An buƙaci malaman addinin Musulunci a Jihar Gombe su rungumi dabarun zamani na tantance gaskiyar bayanai da labarai don yaƙi da labaran ƙarya dana bogi.

 

A wani taron ƙarawa juna sani na yini biyu da kafar yaɗa labarai ta Alƙalanci ta shiryawa malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na jihar, ƙwararru kan yaɗa labarai sun yi magana kan dabarun ganowa, sarrafawa da kuma daƙile labarun ƙarya.

 

Babban editan kafar ta Alƙanci kuma ƙwararre kan tantance labarun bogi, Kwamared Alhassan Bala, yace taron bitar ya mayar da hankali ne kan malaman addinin Musulunci duba da matsayinsu da kuma muhimmiyar rawar da suke takawa a harkokin zamantakewa, musamman a wannan zamani da ake yaɗa bayanai marasa tushe ta dandalolin sada zumunta na zamani.

 

Bala yace “Yayin da Najeriya ke tinkarar babban zaɓen 2027, ganowa da kuma daƙile labarun ƙarya ya zama dole don wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasarmu”.

 

Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Dr Abubakar Shehu Abubakar na uku wanda Alhaji Abubakar Isma’il Abubakar ya wakilta a matsayin uban taron, ya yi ƙira ga malaman addini su bi koyarwar Musulunci wajen tantance bayanai kafin su yaɗa su wa mabiya.

 

Kwararrun ƴan jarida waɗanda suka gabatar da maƙaloli a taron; Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya NUJ Kwamared Alhassan Yahaya da Babban Daraktan Kafar Yaɗa Labarai ta Jihar Gombe (GMC) Dr Ibrahim Isa, sun yi gargaɗin cewa yaɗuwar labaran karya na ƙara zama ruwan dare lamarin dake da wuya a iya daƙile shi kwata-kwata saboda saurin yaɗuwarsu a shafukan sada zumunta.

 

Sun jaddada cewa labarun ƙarya na iya haifar da rikici da tashin hankali a cikin al’umma, da tashin-tashinar siyasa, da kuma tsaiko a harkokin zamantakewa idan ba a magance su yadda ya kamata ba.

 

Ganin matsayinsu a zamantakewa da tasirinsu, kwararrun sun buƙaci malaman addini su rungumi hanyoyin zamani na tantance gaskiyar bayanai da tabbatar da ingancin majiyoyi musamman a shafukan sada zumunta.

 

Wasu malaman addinin da suka halarci taron Sheikh Adam Muhammad Albany Gombe da Kwamared Musliu Aliyu Pindiga, sun bayyana taron a matsayin wanda ya zo akan gaɓa, suna masu cewa sun ƙaru da dabarun tantance bayanai kafin a yaɗa su.

 

Sun jaddada cewa Musulunci ya riga ya bada umarnin a riƙa tabbatar da sahihancin bayanai da majiyoyi kafin a yi aiki da su.

 

A Najeriya, Hukumar Bunƙasa Ci Gaban Fasahar Zamani ta Kasa (NITDA) tace ƙaruwar amfani da shafukan sada zumunta cikin sauri ya ƙara yawan barazanar yaɗuwar labaran bogi a ƙasar.

 

A cewar Cibiyar Bunƙasa Dimokuradiyya da Ci Gaba, bayanai marasa tushe sun taimaka wajen haifar da rikice-rikicen zamantakewa da siyasa da dama a Najeriya a ‘yan shekarun nan.

 

A cewar Hukumar Bunkasa Ilimin Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, fiye da kaso 60 cikin 100 na masu amfani da intanet a duniya sun taɓa cin karo da wani nau’i na labaran ƙarya da na bogi.

 

Masana sun ce magance ƙalubalen yana buƙatar haɗin gwiwa, musamman daga manyan masu ruwa da tsaki kamar shugabannin addini, ƴan jarida, da shugabannin al’umma.

 

Sun jaddada cewa yaɗa bayanai na gaskiya da sadarwa mai ma’ana sune ginshikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent Posts

  • Bauchi Govt Commences Construction of Perimeter Fence in GSSS Gamawa 
  • Gombe Governor Lauds Gender Inclusion as Lafarge Graduates 20 Female Truckers in Ashaka
  • Masana Sun Bukaci Malaman Addini a Gombe Su Rungumi Dabarun Zamani Don Magance Labarun Bogi
  • Fake News: Professionals Charge Gombe Islamic Scholars on Fact-checking Techniques
  • Gombe PDP Denies Faction, Says Party Intact, Affirms Dankwambo as Leader

Recent Comments

  1. A WordPress Commenter on Hello world!

Archives

  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024
  • May 2024
  • April 2024
  • March 2024
  • February 2024

Categories

  • Agriculture
  • Anti Corruption
  • Article/Opinion
  • Cybercrime
  • Economy
  • Education
  • Environment
  • Governance
  • Health
  • Infrastructure
  • News
  • Nutrition
  • Opinion
  • Politics
  • Religion
  • Rural Development
  • Security
  • Tradition
  • Transportation
  • Uncategorized
  • Urban Development
  • Urban Development
  • Women
  • Youths
©2026 Jewel Times | Design: Newspaperly WordPress Theme