By Yunusa Isa, Gombe
Ƙungiyar Hope Springs International da haɗin gwiwar takwararta ta Servants of Hope Initiative, ta gudanar da aikin tiyatar ido ga majinyata fiye da 75 daga ƙananan hukumomin Balanga da Ɓilliri na Jihar Gombe.
Aikin tiyatar idon shine kololuwar aikin jinya kyautan da kungiyoyin suka gudanar tun farko don tallafawa masu ƙaramin karfi dake ƙauyuka da yankunan karkara na ƙananan hukumomin biyu.
Da yake zantawa da manema labarai yayin aikin tiyatar a Kaltungo, babban likitan ido Dokta Gandi Nathan Buba, yace “Yawancin majinyatan tsofaffi ne dake fama da yanar ido”.
Dokta Gandi yace aikin tiyatar wadda ake yi daki-daki, ana sa ran kammala shi cikin ƴan kwanaki.
Da yake yabawa ƙoƙarin da ƙungiyoyin na Hope Springs International da Servants of Hope Initiative suka yi, ƙwararren likitan idon ya buƙaci sauran ƙungiyoyi, da ƴan siyasa da masu hannu da shuni su yi koyi da ƙungiyoyin biyu.
Yace “Da yawa daga cikin majinyatan ba su ma da kuɗin motan zuwa asibiti, ballantana a yi maganar kuɗin tiyata da na magani”.
Yace tallafin ya taimaka wajen farfaɗo da idanun marasa lafiya da dama, waɗanda idan ba a yi mu su tiyatar ba za su kai ga makancewa baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, Daraktan ayyuka na ƙungiyar ta Hope Springs a Afirka Barrister Rambi lbrahim Ayala, yace an zaƙulo majinyatan ne wadanda yanayinsu ke bukatar tiyata, yayin da aka gudanar da aikin tallafin jinyar kyauta a Balanga da Ɓilliri.
Yace ƙungiyoyin biyu suna samun jin daɗi da farin ciki idan suka tallafawa marasa galihu da mabuƙata musamman ta hanyar samar musu muhimman ababen more rayuwa kamar ruwa, da kiwon lafiya da kuma ilimi.
Barista Rambi yace “Burinmu shine mu taba rayuwar ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi daki-daki”.
Wassu da suka ci gajiyar aikin tiyatar idon, sun bayyana matuƙar godiyarsu ga kungiyoyin na Hope Springs International da Servants of Hope Initiative da suka taba rayuwarsu a wannan mawuyacin halin da suke ciki, suna masu addu’ar Allah Ta’ala ya saka musu da mafificin alheri.