Daga Yunusa Isa, Gombe

A ƙoƙarinta na rage zaman kashe wando a tsakanin matasa tare da ƙarfafa musu gwiwa kan dogaro da kai, ƙungiyar rajin samarwa Arewa ci gaba, wato Arewa Development Support Initiative (ADSI), ta shirya taron bada horo na yini biyu kan dabarun hada-hadar kuɗi da tsaro ta yanar gizo ga matasa 100 a Jihar Gombe.

Da take jawabi yayin horon, ko-odinetar ƙungiyar ta ADSI a jihar Hannatu Ahmed Yaro, tace sun shirya horon ne saboda damuwar da suke da ita kan halin da matasa ke ciki na zaman banza, da kuma rage yawan aikata laifuka a jihohin Arewa 19 don samun ci gaban yankin da Najeriya baki ɗaya.

Tace “Za mu horar da su ne kan dabarun hada-hadar kuɗi da yin katin cire kuɗi (ATM card) na monie point wa jama’a, wannan aikin zai sa su samu abun yi su taimaki kansu har su taimaki wassu a rayuwa.”

Hannatu ta ƙara da cewa “ADSI ƙungiya ce ta abokai da ƙawaye masu ra’ayi guda, waɗanda ke da kishin Arewa, kuma masu fafutukar ci gabanta”.

Tace kasancewar ADSI ƙungiya ta ƴan sa kai, kowane ɗan ƙungiyar yana bada gudunmowar aƙalla Naira 2,000 a kowane wata, idan kuɗin suka taru bayan tsawon lokaci sai su yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan da za su kawo ci gaban Arewa da alummarta.

Ta ce a shirin farko da suka aiwatar, sun yi nasarar horar da ɗaruruwan mutane a kan sana’o’i biyar, lamarin da tace ya samar musu abun yi.

Ko’odinetar ta ƙara da cewa bayan kammala horon, za su riƙa sanya ido kan yadda waɗanda suka ci gajiyar shirin suke amfani da ilimi da dabarun da suka koya.

A nasa ɓangaren, Sakataren tsare-tsare na ƙungiyar ta ADSI, Amjad Garba, yace an shirya horon ne don tallafawa marassa galihu a cikin al’umma kan yadda za su bada ta su gudunmawa wajen gina ƙasa.

Da yake ƙira ga waɗanda suka samu horon su yi amfani da ilimin da suka koya don dogaro da kai da kuma ci gaba, Amjad ya roƙi gwamnatoci, da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a su tallafawa shirin don faɗaɗa shi.

Wassu da suka ci gajiyar shirin David Afesomi, da Michael Victor da kuma Mojison Emmanuel sun yabawa ƙungiyar ta ADSI bisa wannan horon, suna masu bada tabbacin cewa horon zai taimaka wajen rage zaman banza a tsakanin matasa. Sun kuma yi ƙira ga sauran jihohi su yi koyi da wannan yunƙuri.

A nasu ɓangaren, wakilan kamfanin Monie Point Nabil Abubakar da Maryam Muhammad, sun yabawa ƙungiyar ta ADSI bisa wannan bada horo, suna addu’ar Allah ya sa shirin ya ɗore.